Qatar za ta ci gaba da kokarin shiga tsakani don kawo karshen yakin da Isra'ila ke yi a Gaza / Photo: AFP / Photo: Reuters

Laraba, 2 ga Oktoban 2024

1633 GMT –– Qatar za ta ci gaba da kokarin shiga tsakani don kawo karshen yakin da Isra'ila ke yi a Gaza

Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya bayyana cewa, Doha za ta ci gaba da kokarin shiga tsakani domin kawo karshen yakin da ake yi a Gaza a daidai lokacin da rikicin yankin ke ƙara ƙamari.

A wani taron manema labarai na hadin gwiwa da Shugaban Ƙasar Iran Masoud Pezeshkian, Sarkin Qatar ya ce, Doha ta yi gargadin ci gaba da ta'azzarar yaƙi a Lebanon tun farkon yakin Gaza.

Shi ma shugaban ƙasar Iran Masoud Pezeshkian da yake nasa jawabin a wajen taron manema labaran na Doha, a kan batun harin makamai masu linzami da aka kai wa Isra'ila, ya ce: - Mun yi ta jiran a samar da zaman lafiya, amma Isra'ila ba ta daina kisan gilla a Tehran da Lebanon ba - Idan suna son ci gaba da hakan, to Isra'ila za ta ga sakamako mafi muni - Idan muka nuna halin ko in kula ga abin da Isra'ila ke yi, za ta ci gaba da yaɗa hargitsi a yankin.

1436 GMT –– Sojojin Isra'ila takwas aka kashe a faɗan da aka gwabza a kudancin Lebanon, kamar yadda rundunar sojin Isra'ila ta fitar a cikin wata sanarwa.

1438 GMT –– Lebanon na bukatar tsagaita wuta nan take: PM

Firaministan Lebanon Najib Mikati ya ce kasar Lebanon na bukatar tsagaita wuta domin kawo karshen kazamin fada tsakanin Isra'ila da kungiyar Hezbollah, yana mai cewa kimanin mutum miliyan 1.2 a fadin kasar Lebanon ne suka rasa matsugunansu sakamakon hare-haren Isra'ila.

"A daina fada. Ba ma bukatar ƙarin zubar da jini, ba ma bukatar ƙarin ɓarna," in ji Mikati a wani taron tattaunawa da kungiyar Amurka Task Force for Lebanon, wata kungiya mai zaman kanta ta Amurka, ta shirya. Ya kara da cewa "Akwai bukatar tsagaita wuta nan take.

0300 GMT — Iran da Isra'ila na yi wa juna barazana; Hezbollah ta daƙile harin ƙasa da Tel Aviv ta kai

Hezbollah ta ce ta yi arangama da sojojin Isra'ila da suka yi kokarin kutsawa cikin kasar Lebanon, tare da kai hari kan sojojin Isra'ila da ke kan iyakar kasar, a cewar sanarwar da kungiyar ta fitar.

Har ila yau, Hezbollah ta ce mayaƙanta sun kai hari kan "wani babban sansanin soji" a Misgav Am da ke kan iyaka da inda aka jibge "rokoki da manyan bindigogi", da kuma inda aka jibe sojoji a wasu wurare uku, inda rukuni daya ke da rokokin Burkan.

A Iran, babban hafsan hafsoshinta ya sha alwashin kai hare-hare kan ababen more rayuwa a fadin kasar Isra'ila idan har aka kai wa kasarsa hari, bayan da Tehran ta harba makami mai linzami kusan 200 kan abokan gabarta, wadda ke yakinta a Zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya tare da kai wa kasar Labanon hari ba ƙaƙƙautawa.

Manjo Janar Mohammad Bagheri ya fada a gidan talabijin na kasar cewa "za a maimaita kai karin da ƙarfi sosai kuma za a kai hari kan dukkanin kayayyakin aikin gwamnati."

Bagheri ya ce Tehran ta kai zuciya nesa bayan da Amurka da EU suka yi alkawarin tsagaita wuta a Gaza biyo bayan kisan da aka yi wa shugaban siyasar Hamas Ismail Haniyeh, ya kara da cewa "a yanzu ba za ta zura ido ba" bayan da Isra'ila ta kashe shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah da Birgediya Janar Abbas Nilforoushan na Iran.

TRT World