Mayakan Pakistan sun kutsa ta sararin samaniyar Iran kuma sun dawo cikin nasara bayan kai wasu hare-hare a maboyar 'yan ta'adda, a cewar kamfanin dillacin labarai na Reuters yana mai ambato majiyar leken asiri ta Pakistan. / Hoto: Reuters Archive

Pakistan ta kaddamar da jerin hare-hare a Iran kan kungiyar ta'addanci ta Balochistan Liberation Army (BLA), bayan ikirarin Tehran na kai hari kan wani sansanin 'yan ta'adda a lardin Balochistan na Pakistan.

Pakistan ta mayar da martani kan hare-haren da Tehran ta kai "ba bisa ka'ida" a Iran da safiyar ranar Alhamis.

''Zan iya tabbatar da cewa mun kai wasu jerin hare-hare kan kungiyoyin 'yan ta'adda masu adawa da Pakistan da aka gano su a Iran,'' a cewar wata majiyar leken asiri da ba a ba ta izininyin bayani ga manema labarai ba ta shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP, inda ta kara da cewa sanarwar gwamnati za ta biyo baya.

"An ji karar fashewar wasu abubuwa a yankuna da dama da ke kusa da birnin na Saravan," a cewar kamfanin dillacin labarai na IR, yana mai ambato wani jami'i daga lardin Sistan-Baluchestan inda birnin yake.

Mutane da dama sun mutu a Iran

Iran ta tabbatar da cewa an kai jerin hare-hare da makamai masu linzami daga Pakistan zuwa wani kauye da ke kan iyaka da lardin Sistan-Baluchistan, kamar yadda wani jami'in tsaron Iran a lardin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na YoungJournalist Club.

Jami'in ya kara da cewa akalla mata uku da kananan yara hudu ne suka mutu a daya daga cikin harin fashewar, inda ya bayyana cewa daga cikin dukka babu wani dan kasar Iran.

Hakan na zuwa ne bayan da Iran ta kai wasu hare-hare kan "maboyar 'yan ta'adda" da ta ce an gano a yammacin ranar Talata a Pakistan - harin da Islamabad ta ce ya kashe yara biyu tare da raunata wasu 'yan mata uku.

Harin makami mai linzami da na jirage marasa matuka sun fada kan mayakan kungiyar Jaish al Adl a Pakistan, kamar yadda gwamnatin Iran ta yi ikirari.

'Maboyar 'yan ta'adda'

Ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ta bayyana cewa kasar yi amfani da karfinta wajen kai wa 'yan ta'addan hari a Iran.

"A safiyar yau Pakistan ta kai jerin hare-haren soji da aka tsara su na musamman a maboyar 'yan ta'adda a lardin Sistan-Baluchistan na kasar Iran," a cewar sanarwar.

Ma'aikatar ta kara da cewa, ''An kashe 'yan ta'adda da dama a yayin wannan aiki na leken asiri.''

Mayakan Pakistan sun kutsa ta sararin samaniyar Iran kuma sun dawo cikin nasara bayan kai wasu hare-hare a maboyar 'yan ta'adda, a cewar kamfanin dillacin labarai na Reuters yana mai ambato majiyar leken asiri ta Pakistan.

Kazalika Islamabad ta jaddada cewa, tana yawan nuna damuwarta game da mafaka da matsugunan da 'yan ta'adda 'yan asalin Pakistan ke samu a Iran.

Ma'aikatar harkokin wajen Pakistan a ranar Laraba ta yi tir da aika-aikar da ta kira da "rashin bin ka'ida da take hakki da kimar 'yancin yankunan Pakistan" kafin ta yi wa jakadanta da ke Iran kiranye tare da dakatar da jakadan Tehran wanda a halin yanzu yake Iran daga komawa kasar.

Tehran da Islamabad suna yawan zargin juna da barin 'yan ta'adda suna ta kai hare-hare daga kowane bangare na yankinsu, kuma da wuya ake iya samun martani.

TRT World