Wasu yaran Falasdinawa na leke ta tafa yayin wani hari da ba bisa ka'ida ba da Isra'ila ta kai a  Turmus Aya kusa da Yammacin Kogin Jordan ranar 22 ga watan Yunin 2023. / Hoto: AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa yara sun fuskanci "tsananin zalunci da take hakkokinsu" a rikice-rikice a shekarar 2022, inda yaki tsakanin Isra'ila da Falasdinawa da kuma rikicin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Somaliya suka jefa yara cikin ukuba, a cewar Asusun Kula da yara na MDD.

A ranar Laraba UNICEF ta bayyana damuwarta kan halin da ake ciki a kasashen Haiti da Nijeriya da Ethiopia da Mozambique da Ukraine, inda Rasha kuwa ta shiga jerin kasashen da MDD ta haramta bibiyar lamarinsu.

"Munanan take hakkokin" sun hada da amfani da yara da ake yi wajen yaki da kashe su da ji musu rauni da lalata da su da sace su da kai hare-hare a makarantu da asibitoci.

Omar Abdi, mataimakin darakta na UNICEF, ya shaida wa Kwamitin Tsaro na MDD cewa an aikata munanan take hakkokin yara fiye da sau 27,000 a bara, inda abin ya karu da 24,000 a kan na 2021, kuma wannan ne karo na farko da adadin ya yi wannan yawan tun bayan da suka soma sa ido kan irin wadannan rahotannin a shekarar 2005.

Yawan rikice-rikicen da "ake damuwa" da su ma ya karu sosai har zuwa 26.

Tun bayan fitar da rahoton, Abdi ya ce wani mummunan yaki ya barke a Sudan, inda ya raba fiye da yara miliyan daya da muhallansu, kuma MDD ta samu rahotannin cewa an kashe daruruwan yara da ji wa wasu da dama raunuka.

Ya kuma ce UNICEF na zaton yawan ya karu a tsakanin yaran Falasdinawa saboda yadda Isara'ila ke ci gaba da kai hare-hare.

Gwamnati da bangarorin da ke yakin ba sa yin komai don kare yara, kuma dole ana bukatar "daukar kwakkwaran mataki," a cewar jami'in na UNICEF.

An sanya Rasha a jerin kasashen da aka haramta amma ba a saka Isra'ila ba

A rahotonsa na farko-farkon shekara da aka fitar a karshen watan da ya gabata, Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya sanya dakarun Rasha a cikin jerin kasashen da MDD ta haramta kan take hakkokin yara sakamakon kashe yara maza da mata da hare-hare kan makaranti da asibitoci a Ukraine.

Amma shugaban na MDD bai sanya a Isra'ila a cikin jerin ba kan take hakkokin yara 1,139 na Falasdinu da ta yi, da suka hada da kashe 54 a bara.

Jakadiya ta musamman kan yara a yayin rikice-rikice, Virginia Gamba ta shaida wa kwamitin cewa munanan take hakkokin yara 27,180 da aka yi a shekarar 2022 sun faru ne a kan yara 18,890 da suka hada da 8,620 wadanda aka kashe ko aka ji musu rauni, da 7,622 da ko dai gwamnatoci ko 'yan ta da kayar baya suka sanya su a cikin yaki, da 3,985 da aka sace da yara mata 1,165, da aka yi wa fyade da yi musu auren dole ko mayar da su bayi ana lalata da su.

MDD ta kuma tantance hare-hare 1,163 da aka kai kan makarantu da 647 da aka kai asibitoci, lamarin da ya karu da kashi 112 daga na 2021, ta ce.

A yayin da kungiyoyin ta da kayar baya ke da alhakin kashi 50 cikin 100 na munanan take hakkokin, Gamba ta ce gwamnatoci su ne manyan wadanda ke aikata kashe-kashen yara saboda hare-haren da ake kai wa kan makarantu da asibitoci.

Gamba ta ce, alal misali, a bara, yara mata uku ne aka yi musu fyaden taron dangi a Sudan ta Kudu "tsawon kwana biyar suna ganin masifa," an kashe yara maza da dama ta hanyar ta da wani bam a wata makaranta a Afghanistan, an sace wata yarinya 'yar shekara 14 tare da kona ta da ranta a Myanmar, sannan wani harin sama da aka kai Ukraine ya yi sanadin cire wa wata yarinya hannaye da kafa.

"Dole mu yi wani abu don kare yaranmu daga bala'o'in yaki," in ji ta.

AP