"Babu lokacin yin makoki, don za a sake samun wasu mace-macen," Mansour ya yi gargaɗi. / Photo: AA

Aƙalla yara 3,000 ne suka mutu a hare-haren da Isra'ila ta ƙaddamar a Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar jakadan Falasɗinu a Majalisar Ɗinkin Duniya.

"Na maimaita, yara 3,000, ƴan mala'ikun yaran da ba su ji ba ba su gani ba aka kashe a Gaza a mako ukun da suka wuce," kamar yadda Riyad Mansour ya faɗa cikin jimami yayin da yake gabatar da jawabi a gaban wani taron gaggawa na Zauren MDD kan rikicin Isra'ila da Falasɗinu.

"Babu lokacin yin makoki, don za a sake samun wasu mace-macen," Mansour ya yi gargaɗi.

Mansour ya ce Falasɗinawa 7,000 aka kashe a hare-haren Isra'ila a Gaza, yana mai cewa kashi 70 cikin 100 na yawan waɗanda aka kashe ɗin mata ne da yara.

"Wannan ne yaƙin da wasun ku suke karewa? Waɗannan munanan laifuka ne. Wannan mugunta ce. Idan har ba ku dakatar da yaƙin don rayukan da aka kashe ba, to ya kamata ku dakatar da shi saboda mu ceto waɗanda suke raye daga a kashe su," ya jaddada.

Har yanzu akwai Falasɗinawa kusan 1,600 da ke maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine, waɗanda ko dai sun mutu ko kuma sun ji raunuka, kuma har yanzu ba a kai ga zaƙulo su ba, ya faɗa.

Mummunan ta'adi

Jakadan ya kuma ce Isra'ila ta lalata fiye da kashi 40 cikin 100 na gidajen da ke Gaza, lamarin da ya raba kusan dukkan al'ummar yankin da gidajensu, inda mutum miliyan 1.4 a yanzu haka suke gararanba, da nufin fitar da su da ga yankin.

Mansour ya kuma ba da misali da kalaman Ministan Harkokin Wajen Isra'ila Eli Cohen a wajen taron Kwamitin Tsaro na MDD, inda yake kira da a saki mutanen da Hamas ke garkuwa da su, yana cewa: "A dawo da su gida."

"Miliyoyin Falasɗinawa ba su da inda za su tafi da za su kira shi gida. Dubban Falasɗinawa kuwa a yanzu ba ma su da sauran dangi da za su gani su runguma. Kuma wannan duk a dalilin wata gwamnati da ta aikata musu hakan," in ji Mansour.

"Ba a ma ta batun ramuwa, abin da kawai ya rage shi ne a yi adalci," ya ƙara da cewa.

An fara rikici a Gaza ne ranar 7 ga watan Oktoba a lokacin da kungiyar Falasdinawa ta Hamas ta kai wasu hare-haren shammata da ban mamaki da suka haɗa da harba rokoki ta ruwa da ta sama da ta ƙasa cikin Isra'ila.

Hamas ta ce ta kai hare-haren ne a matsayin ramuwa kan yawan afka wa Masallacin Ƙudus da kuma kai wa Falasɗinawa hari da sojin Isra'ila da kuma Yahudawa ƴan kama wuri zauna ke yawan yi.

Daga nan ne sai rundunar sojin Isra'ila ta ƙaddamar da nata hare-haren a kan Gaza inda ta dinga afka wa asibitoci da makarantu da ma gidajen mutane.

Mutum miliyan 2.3 da ke Gaza sun rasa ruwa da abinci da magunguna da fetur, sannan an ƙi bayar da damar shigar da kayayyakin agaji zuwa Gazan, ɗan kaɗan ɗin da aka bari ana shigar da su kuma ba su taka kara sun karya ba.

AA