Kimanin yara miliyan 333, yaro daya cikin shida ke rayuwa cikin tsananin talauci a duniya, a cewar wani sabon bincike da UNICEF da Bankin Duniya suka fitar a ranar Larabar nan.
Binciken - wanda aka fitar gabanin babban taron MDD da za a fara ran 18 zuwa 22 ga Satumba, zai hada manyan shugabannin duniya don tattauna batutuwa ciki har da inda aka kwana a tsarin ci gaba mai dorewa na MDD.
Binciken ya yi gargadin cewa ba zai yiwu a iya cimma muradun majalisar da ta sa a gaba na kawar da talauci tsakanin yara ba a shekarar 2030 sakamakon adadin ragin da aka samu.
“Shekara bakwai da suka gabata, duniya ta yi alkawarin kawo karshen tsananin talaucin a tsakanin kananan yara a shekarar 2030. Mun samu ci gaba, wajen nuna cewa da jari da kuma jajircewa sun taka rawa.
"Akwai hanyoyin da za a iya fitar da miliyoyin yara kanana daga halin da ake ciki a lokuta mafi yawa na talauci,” a cewar Babbar Daraktar UNICEF Catherine Russell.
Bincike kan yanayin talauci tsakanin yara da aka saba fitarwa 'Global Trends in Child Monetary Poverty na UNICEF a karon farko ya yi nazari kan tsananin talauci da yara ke fuskanta.
Ya gano cewa tsakanin shekarar 2013 zuwa 2022, adadin yaran da ke rayuwa kasa da dalar Amurka 2.15 a rana ya ragu daga mutum miliyan 383 zuwa miliyan 333, kashi 13 cikin 100 kenan.
''Yankin Kudu da Hamadar Saharar Afirka su suke da kashi 40 cikin 100 na yaran da ke fama da tsananin talauci da kaso mafi yawa a shekara 10 da suka gabata, inda ya tashi daga kashi 54.8 cikin 100 a shekarar 2013 zuwa kashi 71.1 a shekarar 2022,'' a cewar rahoton.
Yawan al'umma da aka kara samu da rashin bin matakan kariya na zamantakewa da kuma matsaloli da aka yi ta samu a duniya ciki har da bullar cutar korona da rikice-rikice da kuma iftila'i na sauyin yanayi duk sun taka rawa wajen karancin adadin da ya ragu na yaran.
''Ko da yake wasu yankunan duniya sun samu ragi na matsanancin yanayin talauci da ake ciki sai dai ban da yankunan Gabas Ta Tsakiya da kuma Arewacin Afirka'' a cewar rahoton.
Yara sun fi fama da talauci
Kashi 50 cikin 100 na yawan al'ummar duniya da ke rayuwa cikin tsananin talauci yara ne, duk kuwa da cewa su ke wakiltar kashi uku cikin 100 na al'ummar duniya baki daya.
Rahoton ya ce, kashi 1 cikin 3 na yara a kasashen da ke fama da tashe-tashen hankula na rayuwa ne a gidajen marasa galihu, idan aka kwatanta da kashi 1 cikin 10 da ke rayuwa a kasashen da ke zaune lafiya.
"Duniyar da yara miliyan 333 ke rayuwa cikin tsananin talauci -- ba wai rashin samun bukatu na yau da kullum ba ne kawai, amma a kare mutuncinsu da ba su damarmaki," in ji Daraktan Bankin Duniya kan yaki da talauci da samar da daidaito Luis-Felipe Lopez-Calva.
"Yana da muhimmanci a samar wa kowane yaro hanyar da ta dace da za a fitar da shi daga kangin talauci - wajen ba shi ingantaccen ilimi da abinci mai gina jiki da kiwon lafiya da kariya a yanayin zamantakewa da kuma tsaro," a cewar Luis- Felipe.