Wasu yara Falasdinawa wadanda suka jikkata a harin da Isra'ila ta kai yankinsu aka kawo su asibitin Shifa da ke Gaza ranar 11 ga Oktoban 2023./ Hoto: AP

Akalla mutum 2,670 aka kashe a Gaza kawo yanzu kuma sama da mutum 750 daga cikinsu yara ƙanana ne, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu a daidai lokacin da aka shiga mako na biyu a hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa yankin da ke karkashin ikonta bayan harin da Hamas ta kai kudancin kasar.

Kutsen da kungiyar Hamas ta yi a Isra'ila wanda ta yi wa suna “Al Aqsa Flood,” ya yi sanadin mutuwar Isra'ilawa fiye da 1,300, lamarin da ya sha suka da kuma Allah wadai daga kasashen duniya.

A bangare guda, ramuwar gayya da Isra'ila take yi kan al'ummar Gaza bai samu wata suka ba daga kasashen yammacin duniya har da kafofin yada labaransu.

Wasu rahotanni da aka gano na karya ne daga baya sun bayyana yadda Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da Shugaban Amurka Joe Biden suka yi ta shelar cewa mayakan Hamas sun fille kawunan yaran Isra'ila 40, lamarin da ya samu suka fiye da hare-haren wuce gona da Isra'ila ta kai kan dimbin al'ummar Gaza.

Daga baya aka tabbatar da wani hoto da aka yada a shafin X na wani jaririn Isra'ila da aka ƙona da kirkirariyar basira AI.

Kusan rabin al'ummar Gaza mutum miliyan 2.3 yara ne 'yan kasa da shekaru 18 wadanda tuni suka fada cikin mummunn yanayi na rashin lafiya da kuma matsala ta kwakwalwa a cikin tsawon shekara 16 da aka kwashe Isra'ila na mamaye da yankinsu, lamarin da a cewar MDD ya mayar da yankin Falasdinu wurin da babu rayuwa.

A cewar kungiyar kare hakkin yara ta kasa da kasa (DCI), da kuma kare hakkin bil'adama ta Falasdinu wacce ta mai da hankali kan hakkokin yara, tun shekarar 2005, manyan hare-hare shida sun kashe akalla yara Falastinawa 1,000.

Ga wasu hotuna da suka yi nuni da irin ta'asar da Isra'ila ta yi kan fararen hula a Gaza.

An kai wasu Falasdinawa da suka jikkata a harin da Isra'ila ta kai yankinsu asibitin Shifa da ke Gaza a ranar Laraba, 11 ga Oktoba, 2023. / Photo: AP

Matsalar Kiwon lafiya

A ranar Larabar data gabata ne kungiyar Doctors Without Borders ta bayar da rahoton cewa kashi 100 na marasa lafiya da aka kawo asibitocinta cikin sa’o’i 24 yara ne.

Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu ta yi gargadi a ranar Larabar kan katsewar ayyukan kiwon lafiya a fadin Gaza, yayin da asibitoci ke fama da rashin isassun gadaje da za su kwantar da wadanda suka jikkata daga harin bama-baman Isra'ila.

"Asibitoci suna fama da karancin gadaje, wadanda suka jikkata da sauran marasa lafiya suna kwanciya ne a kasa yayin da hare-haren Isra'ila ke ƙara tsananta," a cewar sanarwar da ma'aikatar ta fitar.

Ma'aikatar ta ce, ci gaba da katsewar wutar lantarki da ruwa da kuma man fetur da Isra'ila ke yi ''na haifar da hadari ga rayukan wadanda suka jikkata da marasa lafiya, yanayin da ka iya haifar da mummunar matsala ga yanayin samun lafiya da muhalli.''

Ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya sanar da rufe yankin Gaza gaba daya a ranar Litinin, tare da katse hanyoyin samar da ruwa da abinci da wutar lantarki da duk wasu taimako na magunguna da yankin zai iya samu, yana mai jaddada matakin da aka dauka akan Falasdinawa da ya kwatantasu da matsayin "dabbobi".

Wata yarinya Bafalasdiniya ke kuka yayin jana'izar Amir Ganan, wanda aka kashe a harin da Isra'ila ta kai kan gine-gine a Khan Younis a Zirin Gaza, a ranar Talata, 10 ga Oktoba, 2023. / Photo: AP

Matsalar lafiyar kwakwalwa

A cewar wani rahoto na shekarar 2022 da kungiyar Save the Children ta fitar, hudu daga cikin yara biyar a Gaza na fama da matsalar damuwa da bakin ciki da fargaba, sanna fiye da rabin adadin yaran na tunanin kashe kansu.

"Yanzu ne lokacin da ya fi kowane matukar muhimmanci gwamnatin Isra'ila ta janye shingayen da ta yi wa zirin Gaza, domin hukumomin cikin gida da kungiyoyin kasashen waje masu ba da agaji su samu damar shiga yankin don ba da gudunmawarsu tare da hanzarta karfafa ayyukan kare yara da kula da lafiyar kwakwalwarsu," a cewar kungiyar Save the Children.

Sama da yara 800,000 a Gaza ba su taba sanin wata rayuwa ba tare da katangar da aka mamaye su da ita ba.

Wani yaro Bafalasdine da ya jikkata a harin bam da Isra'ila ta kai yana jiran a kawo mishi daukin jinya a wani asibiti da ke sansanin 'yan gudun hijira na Rafah a kudancin zirin Gaza, a Alhamis 12 ga Oktoba, 2023. / Photo: AP

Hukuncin da ya shafi kowa

A cewar Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu, mata da kananan yara a Gaza na fama da kusan kashi 60 cikin 100 na raunukan hare-haren Isra'ila a yankin.

Game da yawan takunkumin da Isra'ila ta sanya kan al'ummar Gaza, Sakatare Janar na hukumar kare hakkin bil'adama ta duniya Amnesty international, Agnès Callamard ta fada a ranar Alhamis cewa: "Hukuncin gama-gari na fararen hular Gaza ya zama laifin yaki - zalunci ne da rashin mutuntaka."

A matsayinta na wacce ta yi mamaya, akwai nauyin da ke rataye a wuyan Isra'ila karkashin dokokin kasashen wajen wajen tabbatar da cewa ta biya duk wasu bukatu na fararen hula a Gaza."

A watan Yunin shekarar da ta gabata, wani kwamiti mai zaman kansa da hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta kafa, wanda ya mayar da hankali kan yankunan Falasdinawa da aka mamaye, ya ce mamaya da kuma nuna wariya su ne ummul aba'isin tashe-tashen hankula da rikici da rashin zaman lafiya da ke ci gaba da faruwa yankin.

Wani dan'uwan wata yarinya da aka kashe a harin da isra'ila ta kai Gaza a ranar Litinin 9 ga watan Oktoba, 2023 ke aihini da juyayin mutuwar. Hoto: AP
TRT World