Hukumomi sun bayar da umarnin rufe wata makaranta a arewacin Jihar Uttar Pradesh wadda rahotanni suka ce malamar makarantar ta bayar da dama ga dalibai su yi ta marin wani dalibi Musulmi.
Hukumomin sun ce makarantar za ta ci gaba da zama a rufe har zuwa lokacin da aka kammala bincike.
An bukaci malamar makarantar ta hallara domin bincike kan lamarin, kamar yadda jami’in ilimi Shubham Shukla ya bayyana a wata sanarwa, inda ya ce za a kwace takardar amincewa da gwamnati ta bai wa makarantar.
An ta ce-ce-ku-ce da nuna bacin rai bayan da bidiyon lamarin wanda ya faru a kauyen Khubbapur da ke Muzaffarnagar ya watsu a ranar Juma’a.
Bidiyon ya nuna dalibin mai shekara bakwai yana tsaye a gaban wani aji inda sauran yaran da ke ajin suka taso suna gaura masa mari har yake kuka.
Malamar wadda ke bin addinin Hindu, an ji tana cewa: “Me kuke yi? Me ya sa ba kwa dukansa sosai?” Sai dai ‘yan sanda a Uttar Pradesh a ranar Litinin sun bukaci ganin mai kafar watsa labarai ta Alt News kuma mai bin diddigi, Mohammad Zubair kan batun bayyana surar yaron da aka mara.
Yadda bidiyo ya jawo ce-ce-ku-ce
Zubair ya yada wani bidiyo a shafinsa na X (wanda a baya ake kira Twitter). Kamar yadda Zubair ya bayyana, ‘yan sanda sun dauki mataki ne bayan da bidiyon ya bazu a shafukan sada zumunta.
Babbar hukumar kare hakkin yara ta National Commission for Protection of Child Rights ta bukaci mutane kan ka da su bayyana yaron ta hanyar yada bidiyon. Daga baya Zubairu ya goge bidiyon.
A bara, ‘yan sandan Delhi sun kama Zubair kan zarginsa da cin zarafi na addini. Haka kuma kuma kungiyoyin Hindu suna ta caccakarsa kan zargin watsa labaran karya da kuma fadin wasu kalaman kiyayya daga malaman Hindu.
Zubair shi ne mutum na farko da ya soma watsa maganganun da shugaban Jam’iyyar Bharatiya Janata ya yi kan Annabi Muhammad (SAW).
Wannan lamarin ya rikide inda ya zama wata babbar matsala a tsakanin Musulmai a kasashe da dama inda suka nuna rashin jin dadinsu kan batun da aka yi game da annabi.