Hukumomin Falasɗinawa da ke kusa da tattaunawar da ake yi sun ce har yanzu ba a kai ga cim ma matsaya ba.  / Hoto: AA

Majiyoyin Falasɗinawa da ke da masaniya kan tattaunawar da ake yi sun ce Amurka da masu shiga tsakani na Larabawa sun samu ci-gaba a yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, amma ci-gaban bai kai yadda za a cim ma matsaya ba.

Yayin da ake ci gaba da tattaunawar a Qatar, sojojin isra’ila sun kai hare-hare a faɗin yankin Falasɗinu da aka mamaye, inda suka kashe aƙalla mutane 17, a cewa cibiyoyin lafiya na Falasɗinu.

Kashe-kashen sun kawo adadin waɗanda hare-haren Isra’ila suka yi sanadiyyar mutuwarsu zuwa 70 a faɗin Gaza cikin sa’o’i 24, kamar yadda ma’aikatar lafiyar yankin ta bayyana.

Qatar da Amurka da Masar suna wani gagrumin yunƙuri na ganin an cim ma matsaya don dakatar da yaƙin da Isra’ila take yi a Gaza da kuma sakin ragowar mutanen da aka yi garkuwa da su kafin Joe Biden ya bar ofis.

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya yi gargaɗin cewa “za a ga balbalin bala’i” idan ba a saki mutanen da aka yi garkuwa da su ba zuwa lokacin da za a rantsar da shi ranar 20 ga Janairu.

A ranar Alhamis, jami’an Falasɗinawa da ke kusa da tattaunawar sun ce, rashin cin ma matsaya kawo yanzu ba ya nufin cewa tattaunawar ba ta kai ko ina ba, kuma wannan ne yunƙurin da ya fi kowanne mayar da hankali kawo yanzu.

“Akwai muhimmiyar tattaunawa da ake yi, masu shiga tsakani da masu tattaunawa suna yin magana sosai akan kowace kalma da kowane batu. An samu nasara idan aka duba yadda aka warware wasu batutuwa da suka zama kiki-kaka a baya, amma dai har yanzu ba a cim ma matsaya ba,” kamar yadda ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ba tare ƙarin bayani ba.

An shafe fiye da shekara guda ɓangarorin biyu sun maƙale a wajen ɗaya kan muhimman batutuwa biyu.

Hamas ta ce za ta saki sauran fursunonin ne kawai idan Isra’ila ta amince da kawo ƙarshen yaƙin ta kuma janye duka sojojinta daga Gaza.

TRT World