Duk da cewa an saba girgizanƙasa a yankin, girgizar ƙasar da aka yi ranar Talata ita ce girgizar ƙasa mafi muni da aka yi cikin shekaru biyar da suka gabata, in ji hukumar CENC. / Photo: AFP

Aƙalla mutum 95 sun mutu bayan wata mummunar girgizar ƙasa ta auku a yankin Tibet na China ranar Talata da safe, in ji gidan talabijin na ƙasar.

"An tabbatar da mutuwar mutum 95 yayin da mutum 130 suka jikkata zuwa karfe uku na rana (ƙarfe 0700 agogon GMT) ranar Talata ," in ji kamfanin dillancin labaran ƙasar China Xinhua.

A baya dai kamfanin ya ce, "Mutum hamsin da uku ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da mutum 62 suka jikkata zuwa misalin ƙarfe sha biyu na rana, bayan girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6.8 ta tayar da ƙaramar hukumar Dingri a birnin Xigaze da ke Xizang ( a Tibet) yanki mai cin gashin kansa da misalin ƙarfe 9:05 na safe ranar Talata."

Bidiyoyin da gidan talabijin na ƙasar China (CCTV) ya wallafa sun nuna gidaje da suka lalace inda katangu suka faɗi bayan girgizar ƙasar.

Girgizar ƙasar mai ƙarfin maki 6.8 ta far ma Dingri ne kusa da kan iyakarta da Nepal ƙarfe 9:05 na safe (ƙarfe 01:05 a agogon GMT), in ji cibiyar bincike kan girgizar ƙasa ta China (CENC). Ita kuwa cibiyar bincike kan ilimin ƙasa ta Amurka ta ce ƙarfin girgizar ƙasar ya kai maki 7.1.

"An tabbatar da mutuwar mutum talatin da biyu kuma 38 suka ji rauni a lokacin da aka yi girgizar ƙasa a ƙaramar hukumar Dingri a birnin Xigaze na Xizang ( a Tibet) yanki mai zaman kansa da misalin ƙarfe 9:05 na safe ranar Talata," in ji kamfanin dillancin labaran Xinhua, inda ya ambato hedikwatar hukumar ba da agajin gaggawa ta yankin.

"Ƙaramar hukumar Dingri da wuraren da ke kewaye da ita sun fuskanci wani motsin ƙasa mai ƙarfi kuma gine-gine da dama asalin inda aka yi girgizar ƙasar sun rufta," in ji rahoton da gidan tabaijin na (CCTV) ya bayar da farko.

Xinhua ta ce "hukumomin na tuntuɓar garuruwa a ƙaramar hukumar domin tabbatar da iya ta’adin da girgizar ƙasar ta yi ".

Yanayi a Dingri yana da tsananin sanyi da ya kai maki -8 a ma’aunin salshiyos kuma zai ragu zuwa ƙasa da maki -18 a yammacin yau, in ji hukumar bincike kan yanayi ta China.

Ƙaramar hukumar Dingri da ke sama-sama a yankin Tibet gida ne ga kimanin mutum 62,000 kuma yana ɓangaren Tsaunin Everest da ke China.

Duk da cewa an saba samun girgizar ƙasa a yankin, girgizar ƙasar ranar Talata ta kasance mafi ƙarfi da aka yi kilomita 200 daga wurin cikin shekara biyar, in ji CENC.

Girgiza sosai

A Kathmandu da wurare kusa da Lobuche a Nepal a cikin dogayen tsaunukan da ke kusa da tsaunukan Evarest su ma girgizar ƙasar da motsin ƙasar da ya biyo bayan girgizar ƙasar ta shafe su.

"Ta girgiza sosai matuƙa a nan, kowa ya farka," in ji wani jami’in gwamnati Jagat Prasad Bhusal a yankin Namche na Nepal, wanda ke kusa da tsaunin Everest.

Amma ba a samu lalacewar abu ko kuma mutuwa ba a wurin kawo yanzu kuma an tura dakarun tsaro, in ji mai magana da yawun ministan cikin gidan Nepal, Rishi Ram Tiwari.

Nepal na zaune ne kan wata muhimmiyar gaɓar ƙasa inda faifayin ƙasa (tectonic plate) na Indiya ke kutsawa cikin faifayin ƙasa (tectonic plate) na Turai da Asiya, lamarin da ya haifar da tsaunukan Himalaya, kuma ana yawan samun girgizar ƙasa.

A shekarar 2015, kusa da mutum 9,000 suka mutu kuma sama da mutum 22,000 suka jikkata a lokacin da wata girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 7.8 ta auku a Nepal, inda ta lalata sama gidaje rabin miliyan.

An ji motsin ƙasa a jihar Bihar ta Indiya, amma ba a samu rahoton jin rauni ba.

Kazalika mutum uku sun mutu yayin da gomman mutane suka ji rauni bayan wata girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 7.0 ta auku a kan iyakar China da Kyrgyzstan a watan Janairun shekarar da ta gabata.

Wata girgizar ƙasar ta watan Disambar shekarar 2023 a arewa maso yammacin China ta kashe mutum 148 tare da raba dubban mutane da gidajensu a lardin Gansu.

Ita ce girgizar ƙasar China da ta fi muni tun shekarar 2014, a lokacin da sama da mutum 600 suka mutu a kudu maso yammacin lardin Yunnan.

TRT World