Goyon bayan Washigton ga ƙawancen ‘yan tawayen SDF a Siriya da YPG ta mamaye na daga manyan abubuwan da ke haifar da saɓani tsakanin Turkiyya da Amurka. / Hoto: AP

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya jaddada cewa Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan “abokinsa” ne da yake girmamawa.

Kalaman nasa sun zo ne yayin wani taron manema labarai a gidansa na Mar-a-Lago a Florida ranar Talata, lokacin da aka tambaye shi dangane da yiwuwar janye sojojin Amurka daga Siriya idan ya karɓi mulki nan gaba a wannan watan.

“Ba zan ce muku haka ba saboda wannan tsari ne na sojoji, sai dai zan ce Turkiyya ce,” a cewar Trump. “Shugaba Erdogan abokina ne, mutum ne da nake so, nake girmamawa. Ina ji shi ma yana girmama ni."

“Amma idan kuka dubi abin da ya faru a Siriya, an raunana Rasha, an raunana Iran. Mutum ne mai dabara, ya tura mutanensa ƙasar ta hanyoyi daban-daban da sunaye daban-daban, kuma sun je sun ƙwace ta,” kamar yadda Trump ya fada.

Gwamnatin Bashar al Assad ta faɗi a watan jiya bayan gamayyar dakarun hamayya sun ƙwace manyan biranen Siriya.

Miliyoyin ‘yan Siriya ciki har da jagororin hamayya, sun koma Turkiyya don tsere wa azabtarwar gwamnatin Assad. Wasunsu a yanzu sun koma don taimakawa a ciyar da ƙasar wacce yaƙi ya ɗaiɗaita gaba.

Amurka tana da sojojin kusan 2,000 a Siriya, inda Washingoton ta jima tana ƙoƙarin halasta kasancewar ƙungiyar ta’addanci ta PPK da takwararta ta Siriya YPG da sunan yaƙar Daesh.

Goyon bayan Washigton ga ƙawancen ‘yan tawayen SDF a Siriya da YPG ta mamaye na daga manyan abubuwan da ke haifar da saɓani tsakanin Turkiyya da Amurka.

TRT World