Mamakon ruwa sama da aka zabga a ƙasar Saudiyya iirn wanda ba a saba gani ba ya jawo mummunar ambaliyar ruwan da ta shafe tituna da unguwanni a fadin biranen da ke ƙasar, yayin da ake sa ran mummunan yanayi zai ci gaba da kasancewa tsawon kwanaki.
A ranar Talata ne Hukumar Kula da Yanayi ta Kasar ta fitar da sanarwar gargaɗin cewa za a yi ambaliya a fadin kasar ciki kuwa har da birane masu tsarki na Makkah da Madina da ke yammacin kasar da ma sauran yankunan da ke gabashi.
Babban birnin ƙasar Riyadh da gundumomin kudu maso yammaci irinsu Aseer da Jazan ma an ba da gargadin cewa hakan zai faru amma ba mai tsanani kamar sauran ba, sai dai duk da haka an bukaci mutane su yi taka tsantsan tare da tsammatar ruwan sama.
Hukumomin agaji na ƙasar da suka haɗa da Red Crescent sun ƙara azama sosai don yin abin da ya dace sakamakon mamakon ruwan saman da aka ba da gargadi a kansa.
Kamfanin dillancin labarai na Saudiyya ya ce hukumar Red Crescent ta tabbatar da cewa a shirye take don tawagogin agajinta su tabbatar da cewa ba a samu tsaiko ba a ayyukan motocin ɗaukar marasa lafiya da kuma ba da agaji ba.
Hukumomin na Saudiyya sun kuma gargadi 'yan ƙasar da cewa su yi taka tsantsan tare da bin dokokin kiyayewa musamman a yankunan da aka yi gargadin cewa lamarin zai munana.
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta buƙci mutane da su guji zuwa wuraren da ke da kwari da kuma yankunan da ruwan saman ke taruwa.
Bidiyoyin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwan sama ke tunƙoro yana shafe motoci da tituna da ma gine-gine saboda yadda yake zuba kamar da bakin ƙwarya da kuma iska mai ƙarfi.