Eliyahu ya nuna “adawa kan bari a shigar da kayan agaji Gaza.”

1540 GMT — Dakarun Hamas sun ce sun lalata tankokin yakin Isra'ila shida

Dakarun Hamas na Al-Qassam sun ce sun lalata tankokin yakin Isra’ila shida da kuma kashe sojojin na Isra’ila da dama.

A wata sanarwa da Hamas din ta fitar ta shafinta na Telegram, ta bayyana cewa dakarunta sun yi amfani da makaman Yassin 105 domin lalata tankar yaki daa a arewa maso yammacin Gaza, sai kuma tankoki biyu a Tal al-Hawa da ke kudancin Gaza, sai wasu tankokin uku a Beit Hanoun da ke arewacin Gaza.

Ana ci gaba da fafatawa tsakanin dakarun Hamas da na Isra'ila. Hoto/Reuters

Zuwa yanzu akalla Falasdiniwa 9,970 Isra’ila ta kashe a Gaza, daga ciki 4,800 yara ne kanana, sannan 2,550 mata ne.

1510 GMT — Jordan ta yi Allah wadai da ministan Isra'ila kan kalaman nukiliya

Kasar Jordan ta yi watsi tare da Allah wadai da kalaman ministan Isra'ila kan amfani da makamin nukiliya a Gaza.

Kasar ta Jordan ta ce wadannan kalaman da ministan ya yi tunzuri ne domin aikata laifukan yaki.

1418 GMT — Saudiyya ta caccaki Isra'ila kan barazanar amfani da nukiliya a Gaza

Kasar Saudiyya a ranar Lahadi ta yi Allah wadai da kalaman da ministan Isra’ila ya yi na shirin amfani da bama-baman nukiliya kan Zirin Gaza da Isra’ilar yi wa kawanya.

“Kin korar ministan nan take daga gwamnati da kuma dakatar da shi ya nuna tsantsar yadda gwamnatin Isra’ila ba ta mutunta bil adama da da’a da addini da shari’a,” kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta bayyana.

Tun da farko a ranar Lahadi, Ministan Al'adun Isra'ila Amichai Eliyahu ya ce akwai yiwuwar su yi amfani da 'bama-baman nukiliya' a Gaza

1310 GMT Chadi ta janye jakadanta daga Isra'ila

Kasar Chadi ta sanar da yi wa jakadanta da ke Isra’ila kiranye sakamakon hare-haren da kasar ke kai wa Gaza.

A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Chadi ta fitar a ranar Lahadi, ta yi Allah-wadai da irin yadda ake samun asarar rayuka a Gaza tare da kira kan a tsagaita wuta.

Haka kuma ta yanke shawarar yi wa jakadanta kiranye daga Isra’ila zuwa N’Djamena domin tattaunawa.

0840 GMT — Wani Ministan Isra'ila ya ce suna da 'zabin' yin amfani da 'bama-baman nukiliya' a Gaza

Ministan Al'adun Isra'ila Amichai Eliyahu ya ce akwai yiwuwar su yi amfani da 'bama-baman nukiliya' a Gaza, kamar yadda kafafen watsa labarai na kasar suka rawaito ranar Lahadi.

Eliyahu, minista na jam'iyya Otzma Yehudit mai tsattsauran ra'ayi, ya ce “daya daga cikin zabin da muke da shi a yakin shi ne mu jefa bama-baman nukiliya a Zirin Gaza,” in ji jaridar Times of Israel.

A yayin da ake hira da shi a wani gidan rediyo, Eliyahu ya nuna “adawa kan bari a shigar da kayan agaji Gaza.”

0157 GMT — An kashe sojojin Isra'ila 345 tun daga 7 ga watan Oktoba

Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta 345 ne suka mutu tun da ta soma kai hare-hare a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba.

Kakakin rundunar sojin Daniel Hagari ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya gudanar ranar Asabar, bayan an kashe karin sojinsu hudu a Gaza.

Ya kara da cewa an kashe sojojin Isra'ila 29 tun daga ranar Talata lokacin da suka kaddamar da hari ta kasa a Gaza.

Hagari ya ce za su ci gaba da yaki a dukkan sassaan Gaza har sai sun wargaza kungiyar Hamas ta Falasdinawa.

Hagari ya kara da cewa an kashe sojojin Isra'ila 29 tun daga ranar Talata lokacin da suka kaddamar da hari ta kasa a Gaza. /Hoto:AA

0100 GMT — Hezbollah ta ce ta kashe sojojin Isra'ila a arewacin kasar

Kungiyar Hezbollah ta ce ta kai hari kan sojojin Isra'ila da dama a cikin wani gida a matsugunin Metula da ke arewacin Isra'ila.

Kungiyar da ke Lebanon ta ce ta kashe sojojin Isra'ila da dama a harin.

Ta kara da cewa harin nata martani ne ga kisan da Isra'ila ta yi wa fararen-hula 'yan kasar Lebanon kwanakin baya.

Rundunar sojin Isra'ila ta yi ikirarin cewa babu wani sojanta da aka jikkata a harin da Hezbollah ta kai sannan ta ce jiragen yakinta sun kai hare-hare da dama a yankunan Hezbollah da ke kudancin Lebanon.

Hezbollah ta kara da cewa harin nata martani ne ga kisan da Isra'ila ta yi wa fararen-hula 'yan kasar Lebanon kwanakin baya. / Hoto: AA / Photo: Reuters

2300 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 51, ta jikkata gommai a sansanin 'yan gudun hijira na Gaza — Faladinu

Isra'ila ta kashe Falasdinawa akalla 51 sannan ta jikkata gommai a harin da ta kai ta sama a sansanin 'yan gudun hijira na Al Maghazi da ke tsakiyar Gaza, a cewar kamfanin dillancin labarai na Falasdinawa WAFA.

Kakakin Ma'aikatar Lafiya ta Gaza, Ashraf al-Qidra, ya ce an kashe mutane da dama ba tare da ya bayar da hakikanin alkaluman wadanda suka mutu ba, sai dai ya kara da cewa gommai sun jikkata kuma suna kwance a dandarin kasa a sashen bayar da agajin gaggawa na asibiti.

Maghazi yana yankin Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza.

Ganau sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa hare-haren sun fada kan gidaje da dama.

"Isra'ila ta kai hari ta sama a gidajen makwabtana da ke sansanin 'yan gudun hijira na Al-Maghazi, an lalata tagogin gidan da ke kusa da nawa," in ji Mohammed Alaloul, mai shekara 37, wani dan jarida da ke aiki da kamfanin dillancin labarai na Anadolu na Turkiyya.

Alaloul ya shaida wa AFP cewa harin ya yi sanadin mutuwar 'ya'yansa Ahmed, dan shekara 13 da kuma Qais, dan shekara hudu, tare da dan uwansa. An jikkata mahaifiyarsa da matarsa da kuma wasu 'ya'yansa biyu.

Gawawwakin yara da Isra'ila ta kashe a harin da ta kai sansanin 'yan gudun hijira na Maghazi, yayin da aka kai su Asibitin Al-Aqsa Martyrs da ke Deir Al-Balah, Gaza ranar 5 ga watan Nuwamba, 2023. / Hoto: AA
AA
TRT World
Reuters
AFP