Firaministan kasar Labanon Najib Mikati, ya yi gargadin cewa za a yi yaki mai cike da rudani a yankin Gabas ta Tsakiya, saboda tsokanar Isra'ila. / Photo: AA / Photo: Reuters

1648 GMT Labanon ta yi gargadin cewa yaki zai iya barkewa a yankin saboda abin da Isra'ila ke yi

Firaministan kasar Labanon Najib Mikati, ya yi gargadin cewa za a yi yaki mai cike da rudani a yankin Gabas ta Tsakiya, saboda tsokanar Isra'ila.

Sanarwar da majalisar ministocin kasar ta fitar ta ambato Mikati yana fada a yayin ganawarsa da Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya David Cameron a Beirut cewa, "Ci gaba da tsokanar da Isra'ila ke yi a kudancin Labanon na iya haifar da tabarbarewar al'amura da kuma barkewar yakin basasa a yankin."

"Kofar dakatar da yakin Gaza ta fara ne da tsagaita wuta, sannan kuma a ci gaba da yin shawarwari kan yadda za a cimma matsaya kan tsarin kasashe biyu da bai wa Falasdinawa 'yancinsu," in ji Mikati.

1313 GMT Masar na jiran martani kan shirin kawo karshen zubar da jini a Gaza: Alkahira

Masar ta tabbatar da cewa ta gabatar da wani tsari na kawo karshen yakin da Isra'ila ke yi a Gaza wanda ya ƙunshi matakai uku da za su kawo tsagaita wuta, ta kuma ce tana jiran martani kan shirin.

Shugabar Hukumar Yada Labarai ta Masar din, Diaa Rashwan, a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce Masar za ta ba da cikakkun bayanai kan shirin da zarar an samu wadannan martani.

Shawarar wani yunƙuri ne na "na kusantar da ra'ayi tsakanin dukkan bangarorin da abin ya shafa, don dakatar da zubar da jinin Falasɗinawa da cin zarafi a kan Gaza da maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin," in ji shi.

1249 GMT An kashe mutum 240 cikin awa 24 a Gaza — Ma'aikatar Lafiya

Gaza

Aƙalla Falasɗinawa 210 aka kashe a hare-haren Isra'ila cikin 24 da suka wuce, lamarin da ya sa yawan Falasɗinawan da suka mutu tun fara yaƙin ya kai 21,320, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Gaza.

Ma'aikatar ta kuma ƙara da cewa mutum 55,603 ne suka jikkata sun bayan fara yaƙin da Isra'ila ke yi a yankin da aka yi wa ƙawanyar.

0700 GMT — Isra'ila ta kashe mata da kananan yara Falasdinawa a sabbin hare-haren da ta kai Gaza

Jiragen yakin Isra'ila sun kashe Falasdinawa akalla 50 a hare-haren da suka kai Beit Lahia, Khan Younis da Maghazi, a cewar Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Falasdinu.

Tun da farko a yau, kamfanin dillancin labaran Wafa na Falasdinu ya ambato wasu majiyoyi suna cewa Isra'ila ta kashe akalla fararen-hula bakwai, galibinsu kananan yara da mata a hari ta sama da jiragen yakinta suka kai sansanin 'yan gudun hijira da ke tsakiyar Gaza.

Mutane da dama sun jikkata yayin da jiragen yakin Isra'ila suka yi luguden wuta a wani gida da ke sansanin 'yan gudun hjira na Nuseirat.

Kazalika an bayar da rahoton mutuwa da jikkatar mutane a luguden wutar da jiragen yakin Isra'ila suka yi a wani gida a yankin Al Zuwaida da ke tsakiyar Gaza.

Haka kuma Isra'ila ta kai hare-hare a tsakiyar birnin Khan Younis da ke kudancin Gaza, in ji Wafa.

0128 GMT — Rasha ta yi kira da a kawo karshen zaluncin da Falasdinu ke fuskanta a tarihi

Rasha ta ce barkewar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya ya samo asali ne sakamakon gazawar manufofin harkokin wajen Amurka da aka dade ana yi, tare da yin kira da a kafa kasar Falasdinu.

A cikin kalamansa ga kamfanin dillancin labarai na TASS, ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya yi kira da a sassauta rikicin yankin Gabas ta Tsakiya, yana mai cewa "ba za a amince da shi ba", wanda ayyukan ta'addanci ne.

An ambato shi yana cewa "Yana da matukar muhimmanci a kawar da munanan yanayin tashe-tashen hankula tare da kawar da zaluncin da al'ummomi da dama na Falasdinawan suka sha wahalarsa."

“Ta hanyar yin hakan ne kawai za a iya samun kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya baki daya."

Makircin Ƙasashen Yammacin Duniya da mamayarsu ke ƙarewa ne ke da alhakin jefa duniya cikin rudani, in ji Lavrov a wata hira da aka wallafa a ranar Alhamis.

Wata mata tana kuka a asibitin Nasser da ke Khan Younis a kudancin Gaza sakamakon kisan dan uwanta ranar 27 ga watan Disamba, 2023. / Hoto: AA

0103 GMT — 'Fannin lafiyar Gaza na fuskantar bala'i'

Babban jami'in agaji na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi game da bala'in kiwon lafiya a Gaza, yayin da da ƙyar asibitoci ke iya yin ayyukan da suka kamata na kula da jama'a sakamakon yaƙin da ake yi.

Gaza hospitals

"Asibitoci suna aiki da ƙyar. Cututtuka suna yaɗuwa cikin sauri a cikin matsugunai masu cunkoso. Daruruwan mutanen da ke fama da raunukan yaƙi ba sa iya samun kulawa.

"Fannin lafiyar Gaza na fuskantar bala'i, "in ji Martin Griffiths, Mataimakin Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin jinƙai da agajin gaggawa, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da abokan huldarta sun kai man fetur da sauran muhimman kayayyaki ga asibitoci biyu a arewacin Gaza da kudancin Gaza a wannan makon, in ji hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya a cikin wata sanarwa.

Darakta Janar na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi kira ga kasashen duniya da su “dauki matakan gaggawa don kawar da mummunan bala’in da al’ummar Gaza ke fuskanta, tare da yin illa ga ma’aikatan jinƙai da suke taimaka wa mutanen da ke fama da munanan raunuka, da matsananciyar yunwa, da kuma hadarin kamuwa da cututtuka,” a cewarsa.

TRT Afrika da abokan hulda