Wata Kotun Daukaka Kara a Pakistan ta dakatar da hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru uku da aka yanke wa fitaccen tsohon Firai Ministan kasar Imran Khan, sakamakon cin hanci da rashawa, a cewar lauyoyinsa da kuma jami'an kotun.
Ana sa ran hukuncin zai bai wa Khan, mai shekaru 70 damar tsayawa takara a zaben 'yan majalisar dokoki da ke tafe, duk da cewa za a ci gaba da yi masa shari'a.
Khan dai ya musanta zargin da ake masa, yana mai dagewa kan cewa bai karya wata doka ba.
Duk da hukuncin babbar kotun Islamabad na bayar da belin Khan, har yanzu ba a san ko za a sake shi ba saboda karin wasu tuhume-tuhume da aka gabatar akansa tun bayan hambarar da shi da aka yi ta hanyar jefa kuri'ar raba gardama a majalisar dokokin kasar a watan Afrilun 2022.
A farkon watan nan ne kotu ta yanke wa Khan hukunci zaman gidan yari bayan samunsa da laifin boye wasu kadarori da kuma zargin sayar da kayan gwamnati ba bisa ka’ida ba a lokacin da yake rike da mulki.
"Imran Khan ya sake samun damar jagorantar jam'iyyarsa ta Pakistan Tehreek-e-Insaf bayan umarnin kotu na yau," a cewar Babar Awan, wani babban lauyan Khan, a zantawarsa da manema labarai bayan sanarwar hukuncin da kotu ta yi.
A farkon watan Agusta nan ne, hukumar zaben Pakistan ta haramtawa Khan tsayawa takara na tsawon shekaru biyar.
A dokar kasar ba a yarda wani da aka samu da laifi ya jagoranci wata jam'iyya ko ya tsaya neman wani matsayi ko kuma rike ya mukamin gwamnati ba.