Hukuncin kisan na zuwa ne kasa da mako guda bayan da kasar Singapore ta zartar da hukuncin kisa kan mace ta farko a cikin shekaru kusan 20 saboda kama ta da laifin safarar miyagun kwayoyi duk kuwa da Allah wadai da kungiyoyin kare hakkin bil adama suka yi. / Hoto:Reuters

Kasar Singapore ta zartar da hukuncin kisa kan wani mutum mai shekaru 39 da aka samu da laifin safarar hodar ibilis.

Hukuncin kisan da aka aiwatar ta hanyar rataya shi ne karo na uku da aka yi cikin mako guda kacal kuma na biyar a Singapore a wannan shekarar, a cewar hukumomi.

An yanke wa mutumin hukuncin ne a ranar Alhamis, a cewar sanarwar da hukumar da ke yaki da safarar miyagun kwayoyi ta kasar (CNB) ta fitar.

An yanke wa Mohamed Shalle Adul Latiff hukuncin kisa ne saboda samunsa da kusan giram 55 na hodar ibilis "don fataucin su" a shekarar 2019.

A cewar takardun kotu, Mohamed Shalle ya yi aiki a matsayin direban jigilar kaya kafin a kama shi a shekarar 2016. A yayin zaman shari’arsa, ya yi ikirarin cewa a zatonsa yana hanyar kai tabar sigari ne ga wani abokinsa da yake bi bashi.

Yanzu haka ya zama fursuna na 16 da aka aika zuwa gidan rataya tun da gwamnati ta dawo da aiwatar da hukuncin kisa a watan Maris na 2022 bayan ta dakatar da shi tsawon shekaru biyu sakamakon bullar cutar korona.

Kazalika hukuncin kisan na zuwa ne kasa da mako guda bayan Singapore ta zartar da hukuncin kisa kan mace ta farko a shekaru kusan 20 saboda kama ta da laifin safarar miyagun kwayoyi duk kuwa da Allah wadai da kungiyoyin kare hakkin bil adama suka yi ta yi kan lamarin.

Matsi daga kasashen duniya

An zartar da hukuncin kisa kan Saridewi Binte Djamani, 'yar asalin kasar Singapore mai shekaru 45 a ranar Juma’a bisa laifin safarar kimanin giram 30 na hodar ibilis.

Haka kuma an rataye wani magidanci mai suna Mohd Aziz bin Hussain, mai shekaru 57, a duniya kwanaki biyu da suka gabata bisa laifin safarar kimanin giram 50 na hodar ibilis.

A makon jiya Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir tare da Alla-wadai kan hukuncin ratayan da ake yi inda ta yi kira ga kasar Singapore da ta dakatar da wannan danyan hukunci na kisa.

Duk da karin matsin lamba da kasashen duniya ke yi kan batun, Singapore ta dage kan cewa hukuncin kisa na da matukar tasiri wajen dakile ayyukan safarar miyagun kwayoyi da ake yi a kasarta.

Cibiyar hada-hadar kudade tana da wasu dokoki masu tsauri a duniya inda fataucin fiye da giram 500 na hodar ibilis ko fiye da giram 15 na hodar ka iya haifar da hukuncin kisa.

TRT World