Kasashen Denmark da Sweden sun fuskanci tashin hankali kan kona Kur’ani mai tsarki, lamarin da ya janyo bacin rai daga kasashen Musulmai. Hoto: AP

Gwamnatin Denmark za ta gabatar da wata doka da za ta haramta kona Alkur’ani a wuraren taron jama’a, wannan na daga cikin kokarin da kasar ke yi wajen rage yawan tashe-tashen hankula da ke kara ta’azzara tsakanin kasashen Musulmai da dama ciki har da Turkiyya kan batun.

"Gwamnati za ta gabatar da dokar da ta haramta duk abun da ya saba ka'ida ko mutuncin addinin al'ummomi," a cewar Ministan Shari'ar kasar, Peter Hummelgaard a yayin zantawarsa da manema labarai a ranar Juma'a.

"Dokar za ta sa a hukunta mai laifin da a misali ya kona Al-Kur'ani ko Bible ko kuma Attaura a bainar jama'a," in ji shi.

Wadanda suka karya doka za su fuskanci hukuncin biyan tara da daurin shekaru biyu a gidan yari.

Sanarwar ta zo ne kwana guda bayan da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta gayyaci jami'an hulda da jama'a na kasar Denmark a Ankara, kan batun wulakanta Kur'ani da ake yi a kasashensu.

An dauki matakin ne bayan kona Kur'ani mai tsarki a birnin Copenhagen na kasar Denmark a kwanaki hudu a jere cikin wannan mako.

Zuwa wannan lokaci Turkiyya ta gayyaci jakadan Denmark har sau biyar cikin wannan wata kan batun.

Matakin da gwamnatin tsakiyar ta gabatar zai kara fadada dokar hana kona tutocin kasashen waje da Denmark ta yi wajen "hana tozarci ga duk wani abu da ya shafi mutuncin addini da al'umma," a cewar Hummelgaard.

“Kudirin dokar zai sa a hukunta mai laifi, misali, kona Al-Kur’ani ko Littafi Mai Tsarki a bainar jama’a. Zai mayar da hankali ne kan bainar jama'a ko kuma yada laifin a cikin al'umma, "in ji Hummelgaard.

A ‘yan makonnin nan dai an fuskanci tashe-tashen hankula a kasashen Denmark da Sweden inda aka yi ta kona Kur’ani ko kuma cin mutuncin littafin, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce daga kasashen Musulmai, inda suka bukaci gwamnatocin kasashen na yankin Turai su dauki mataki wajen dakatar wannan mummunan al'amari.

TRT World