Ya kuma yi gargadin cewa za a ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa da ke kan hanyar zuwa Isra'ila. / Photo: AFP

1530 GMT — Mayakan Houthi ne Yeman sun sha alwashin ci gaba da kai hare-hare a Bahar Maliya bayan harin da Amurka ta jagoranci kai musu

Babban mai shiga tsakani na 'yan tawayen Houthis na kasar Yemen ya ce matsayin kungiyar bai sauya ba tun bayan harin da jiragen yakin Amurka da Amurka ke jagoranta suka kai kan matsugunanta.

Ya kuma yi gargadin cewa za a ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa da ke kan hanyar zuwa Isra'ila.

A makon da ya gabata ne jiragen yakin Amurka da na Burtaniya da jiragen ruwa suka kaddamar da hare-hare da dama a fadin kasar Yemen, a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da 'yan Houthi suka kai kan safarar jiragen ruwa a Bahar Maliya, wanda 'yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran suka jefa a matsayin martani ga farmakin da Isra'ila ke kaiwa Gaza.

Mohammed Abdulsalam ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Litinin cewa, za a ci gaba da kai hare-hare don dakatar da jiragen ruwa na Isra'ila ko kuma wadanda ke kan hanyar zuwa tashar jiragen ruwa na Falasdinu da ta mamaye.

1500 GMT — Makami mai linzami ya harbo wani jirgin ruwan Amurka a Gabar Tekun Yemen

Wani makami mai linzami da aka harba daga Yemen ya kai hari kan wani jirgin ruwa mallakar Amurka a Mashigin Tekun Aden, kamar yadda wasu kamfanoni masu zaman kansu na tsaro suka shaida wa kamfanin dillacin labarai na Associated Press.

Ambrey da Dryad Global sun bayyana jirgin a matsayin Eagle Gibraltar, wani babban jirgin jigilar kaya mai dauke da tutar Tsibirin Marshall.

Jirgin mallakin Eagle Bulk ne, wani kamfani mai zaman kansa a Stamford, Connecticut wanda aka yi cinikinsa a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta New York. Kamfanin bai amsa buƙatun da aka aika masa don yin tsokaci ba.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, ko da yake ana zargin 'yan Houthi na Yaman.

Rundunar sojojin ruwan Amurka da ke Bahrain ta 5th Fleet ba ta amsa bukatar jin ta bakinta ba.

1219 GMT — Iran ta nemi a bi hanyar diflomasiyya don kawo ƙarshen yaƙin Isra'ila a Gaza

Hossein Amirabdollahian ya fadi hakan ne a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da ya yi da takwaransa na Indiya a Tehran.

Ministan Harkokin Wajen Iran ya ce Amurka ba za ta iya yin kira da a yi taka-tsan-tsan ba yayin da take goyon bayan yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, yayin da ya yi kira da a warware yaƙin da ake yi ta hanyar diflomasiyya.

Hossein Amirabdollahian, a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da aka watsa ta talabijin tare da takwaransa na Indiya a Tehran, ya yi kira ga jami'an Amurka "ka da su danganta tsaro da muradun Amurka da makomar firaministan Isra'ila da ke faduwa."

0902 GMT Hare-haren Isra'ila sun kashe Falasdinawa sama da 24,000 a Gaza

Aƙalla mutum 24,100 ne suka mutu a Gaza a cikin tsawon wata uku na mummunan yaƙin da Isra'ila ke yi a yankin da aka yi wa ƙawanya, a cewar ma'aikatar lafiya ta Falasdinu.

Wata sanarwa ta ce yawan wadanda suka mutun ya hada da mutum 132 da aka kashe a cikin awa 24 da suka wuce, yayin da har yanzu akwai mutane da dama da suka maƙale a ƙarƙashin baraguzai, kazalika mutum 60,834 ne suka jikkata tun 7 ga watan Oktoban 2023.

0858 GMT — Isra'ila ta kashe karin Falasdinawa biyar a Gabar Yamma da Kogin Jordan

Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta bayyana cewa Isra’ila ta kashe Falasdinawa biyar a Gabar Yamma da Kogin Jordan.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce akwai wani yaro dan shekara 14 wanda ya rasa rayuwarsa sakamakon wutar da Isra’ila ta bude a sansanin ‘yan gudun hijira na birnin Jericho.

Kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar WAFA ya bayyana, dakarun na Isra’ila sun harbi yaron a kirji a yayin da suka kai hari sansanin.

0828 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 60 a cikin dare daya

Isra'ila ta kashe sama da Falasdinawa 60 a a cikin dare guda a Gaza a sakamakon hare-haren da take ci gaba da kaiwa, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu ta tabbatar.

Ma'aikatar ta bayyana cewa akwai gomman mutane wadanda aka raunata a sakamakon munanan hare-haren da Isra'ila ke kaiwa na atilare a cikin Gaza.

Hare-haren sun fada a cikin biranen Khan Younis da Rafah duka wadanda suke kudanci, da kuma wasu wurare da ke cikin Zirin Gaza, kamar yadda ofishin watsa labaran ya tabbatar.

AA
AFP
AP
Reuters