Guterres ya yi maraba da tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, amma ya ce babu inda ke da aminci a Gaza. / Hoto: AA

17:00 GMT — Kayan agajin da ake kai wa Falasdinawa ba sa isarsu: Sakatare Janar na MDD

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa sama da mazauna yankin Gaza miliyan biyu ba za su iya samun isasshen agaji a Zirin Gaza ba, yayin da ya bukaci a tsagaita wuta.

Guterres ya kara da cewa, "Matakin agajin da ake ba Falasdinawa a Gaza ba ya isa wajen biyan bukatu da yawa na mutane sama da miliyan biyu, kuma duk da cewa an ara yawan man fetur da aka bari a kai Gaza, har yanzu bai isa ba don ci gaba da gudanar da ayyukan yau da kullum," kamar yadda ya shaida wa taron Kwamitin Tsaro na MDD kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya.

"Fararen hula a Gaza na bukatar a ci gaba da kai musu agajin jinai na ceton rai da kuma fetur a cikin yankin da kuma fadin yankin. Ana tsananin bukatar amintacciyar hanyar shigar da agaji ga dukkan masu bukata," in ji shi.

Guterres ya yi maraba da tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, amma ya ce babu inda ke da aminci a Gaza.

1400 GMT — Shugaba Erdogan ya sha alwashin bin hanyar diflomasiyya don tsagaita wuta da sakin fursunoni a Gaza

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa, Turkiyya za ta ƙara ƙaimi wajen ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma samar da mafitar tsagaita wuta ta dindindin a Gaza.

A jawabin da ya yi wa kungiyar 'yan majalisu ta jam'iyyarsa ta AK Party a ranar Laraba, Erdogan ya ce firaministan Isra'ila Netanyahu ya aikata daya daga cikin "manyan zalunci" na ƙarni, kuma ya shiga tarihi a matsayin "mai kashe mutanen Gaza."

Ya kuma ce kalaman baya-bayan nan da gwamnatin Netanyahu ta yi suna rage fatan da ake da shi na tsagaita wuta mai dorewa a Gaza, in ji shi.

Dangane da taimakon jin kai da Turkiyya ke yi a Gaza, Erdogan ya ce wani jirgin ruwan agaji na biyu dauke da tan 1,500 na kayayyakin agaji zai tashi a ranar Laraba.

1145 GMT — Akwai yiwuwar Hamas da Isra'ila su kara tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta

An yi musayar fursunoni da dama sakamakon wannan yarjejeniyar tsagaita wutar. / Hoto:Reuters. Photo: Reuters

Akwai yiwuwar a tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni zuwa karin kwana daya ko biyu tsakanin Hamas da Isra’ila wadda za ta kawo karshe a ranar Alhamis da safe, kamar yadda kafar watsa labarai ta kasar Isra’ila ta ruwaito.

A yayin wani taro da aka gudanar a birnin Doha, wanda ya samu halartar wakilai daga kasashen Qatar da Masar da Isra’ila da Amurka, sun tattauna yiwuwar tsawaita yarjejeniyar, kamar yadda kafar watsa labarai ta Isra’ila ta ruwaito inda take alakanta hakan da wata sanarwa wadda hukumomin Isra’ilar suka fitar a ranar Talata.

Sai dai babban kalubalen a halin yanzu shi ne bukatar da Hamas din take da ita ta Isra’ila ta tsagaita wuta baki daya.

0950 GMT — Jirgin Turkiyya dauke da tan takwas na magunguna don mutanen Gaza ya kama hanyar zuwa Masar

Jirgin sojin Turkiyya dauke da tan takwas na magunguna da kayayyakin asibiti wanda zai je Gaza ya bar filin jirgin lardin Kayseri na Turkiyya zuwa Masar.

Ma’aikatan lafiya tara ne ke cikin jirgin wanda ya bar filin jirgin Kayseri da misalin 8:00 na same wato 0500 agogon GMT.

Turkiyya ta aika da taimako ba adadi zuwa Gaza tun bayan da aka soma wannan yaki. / Hoto:AA

Ana sa ran jami’an lafiyan za su kula da wadanda suka samu rauni tare da hadin gwiwar jami’an lafiya na Masar.

0920 GMT Karin motoci 200 na agaji sun shiga Gaza ta Rafah

Jimlar manyan motoci 200 ne suka ketara da kayayyakin agaji cikin Gaza a ranar Talata ta mashigar Rafah da ke iyaka da Masar.

Kayayyakin agajin da aka shigar da su sun hada da ruwa da abinci da magunguna, kamar yadda Wael Abu Mohsen wanda shi ne daraktan mashigar ta Rafah ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Ya kara da cewa ana sa ran wasu karin motocin agajin su kara shiga a cikin wasu sa’o’i masu zuwa, kamar yadda ya kara da cewa.

An kai motoci dauke da kayan agaji da dama zuwa Gaza tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwana hudu. / Hoto: Reuters

0657 GMT — Gaza tana fuskantar tsananin karancin abinci – World Food Programme

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya wato World Food Programme (WFP) ya yi gargadi cewa akwai yiwuwar Gaza ya yi fama da matsanancin karancin abinci, yana mai jaddada cewa abincin da ake kai wa bai isa ba wurin magance matasalar yunwa a yankin.

"Akwai matukar yiwuwar mutanen Gaza, musamman mata da kananan yara, za su fuskanci matukar karancin abinci idan Shirin WFP bai ci gaba da samar da abinci ba," in ji wata sanarwa da Shirin na WFP ya fitar.

" WFP na matukar bukatar abincin da zai bai wa fiye da mutum 120,000 a Gaza a matakin farko," a cewar sanarwar.

Samer Abdeljaber, wakilin WFP kuma darakta a yankin Falasdinu, ya ce tawagarsa ta ga yadda mutane suke cikin "yunwa da bala'i da rushewar muhallansu" kuma ba su samu agaji ko daya ba cikin makonnin da suka gabata.

0230 GMT — Kungiyar Hamas ta gayyaci Elon Musk zuwa Gaza don ya ga barnar da Isra'ila ta yi

Gaza

Wani babban jami'in Hamas ya gayyaci hamshakin mai arzikin nan na Amurka Elon Musk zuwa yankin Gaza da aka yi wa kawanya don ya ga girman barnar da hare-haren Isra'ila suka jawo da yadda hakan ya yi asarar rayukan Falasdinawa 15,000, mafi yawansu mata da yara.

"Muna gayyatarsa ​​[Elon Musk] ya ziyarci Gaza don ganin girman kisan kiyashi da halakar da aka yi wa al'ummar Gaza, tare da bin ka'idodin haƙiƙa da gaskiya," kamar yadda babban jami'in Hamas Osama Hamdan ya fada a wani taron manema labarai a birnin Beirut ranar Talata.

A ranar Litinin ne ma'abota shafukan sada zumunta suka dirar wa attajiri Elon Musk saboda nuna goyon baya ga wani sako da aka wallafa na nuna kyamar Yahudawa, yana zagaya wurin da kungiyar Hamas ta kai wa Isra’ila harin ba-zata tare da bayyana aniyarsa ta yin duk abin da ya dace domin daƙile yaɗuwar ƙyama.

Kungiyar Hamas ta gayyaci Elon Musk zuwa Gaza don ya ga barnar da Isra'ila ta yi ." /Hoto: AA

2206 GMT — CIA, Mossad, Qatar suna tattaunawa don tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza - Kafofin yada labaran Isra'ila

Kafar watsa labarai ta gwamnatin Isra'ila KAN ta rawaito cewa an fara tattaunawa a kasar Qatar kan wata sabuwar yarjejeniya ta tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin Gaza da Isra'ila ta yi wa ƙawanya.

KAN ta ce dakatarwar za ta hada da sakin dukkan fursunonin Isra'ila a Gaza da aka yi wa ƙawanya, ciki har da sojoji, da kuma sakin Falasdinawan da Isra'ila take tsare da su a gidajen yari, har da wasu da aka samu da laifin kisan 'yan Isra'ila.

Falasdinawa a ko da yaushe suna yin watsi da tuhumar da gwamnatin 'yan mamaya da kotuna ke yi musu.

KAN ta ce kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana amincewarta da fadada abin da sabuwar yarjejeniyar za ta ƙunsa amma ta kara da cewa ta bukaci da a tsagaita wuta, wanda har yanzu Isra'ila ta ƙi amincewa da shi.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun ruwaito cewa, shugaban hukumar leken asirin Isra'ila Mossad, David Barnea da shugaban hukumar leken asirin Amurka (CIA) William Burns, da daraktan hukumar leken asirin Masar (GIS) Abbas Kamel da firaministan Qatar Sheikh Mohammed bin Abdul Rahman Al Thani ne suke halartar tattaunawar.

TRT Afrika da abokan hulda