Twitter ya yi barazanar gurfanar da Meta a gaban kuliya awanni kadan bayan kamfanin wanda ya mallaki Instagram ya bude manhajar Threads.
An bude manhajar ce da zummar yin gogayya da Twitter wadda hamshakin attajirin nan Elon Musk ya mallaka.
A wata wasika ya lauyan Musk, Alex Spiro, ya aike wa shugaban Meta, wadda jaridar intanet ta Semafor ta soma wallafawa sannan kafafen watsa labaran Amurka su ma suka buga ranar Alhamis, ya zargi Mark Zuckerberg da "yin amfani da sirrikan kasuwancin Twitter da kuma kayansa ba bisa ka'ida."
Wasikar ta zargi Meta da daukar wasu tsofaffin ma'aikatan Twitter aiki wadanda "suka ci gaba da samun damar kwasar sirrikan kasuwanci na Twitter da kuma wasu manyan bayanan sirri."
Da yake karin bayani game da wasikar, Elon Musk ya wallafa sakon Twitter da ke cewa "gasa aba ce mai kyau, amma laifi ne a yi cuta."
Ana kallon Threads a matsayin babban shafin sada zumunta da ke barazana ga Twitter. Tun bayan kaddamar da shi ranar shida ga watan nan, shafin ya samu miliyoyin mutane a kasashen duniya fiye da 100.
Cikin awanni kadan bayan bude shi, fiye da mutum miliyan 30 sun yi rajista da Threads, kamar yadda Zuckerberg ya bayyana ranar Alhamis.
Kaddamar da shafin na Threads ya kara fito da zazzafar adawar da ke tsakanin Zuckerberg da Musk wadanda suka dade ba sa ga-maciji-da-juna.
A sakon da ya fitar a Twitter irinsa na farko cikin shekaru da dama, Zuckerberg ya wallafa hoton gizo-gizo da ke nuna kamanceceniyar da ke tsakanin Threads da Twitter.