A cewar  Kepios, Facebook ne ke ci gaba da zama shafin soshiyal midiya da aka fi amfani da shi, daga nan sai YouTube, WhatsApp da Instagram. / Hoto: Reuters

Kusan mutum biliyan biyar, wato fiye da kashi 60 cikin dari na al'ummar duniya ne suke amfani da soshiyal midiya, a cewar wani sabon bincike.

Hakan na nufin an samu karin kashi 3.7 cikin dari na masu hawa kan shafukan sada zumunta idan aka kwatanta da bara, in ji kididdigar da Kepios, wani kamfani da ke bibiyar yadda ake amfani da shafukan soshiyal midiya.

Kamfanin ya fitar da rahoton ne ranar Alhamis.

"Masu amfani da soshiyal midiya sun ci gaba da karuwa a watanni 12 da suka gabata, inda aka samu karin mutum miliyan 173 na sabbin masu amfani da wadannan manhajoji daga wancan lokaci zuwa yanzu," a cewar Kepios.

Sai dai Kepios ya ja hankali cewa mai yiwuwa adadin masu amfani da soshiyal midiya ya fi wanda ya fitar saboda wasu abubuwa da suka hada bude shafi iri guda fiye da daya.

Nahiyoyin da suka fi amfani da soshiyal midya

Akwai babban bambanci na amfani da soshiyal midiya tsakanin nahiyoyi. Mutum daya ne kacal cikin ko wadanne mutum 11 suke amfani da shafukan sada zumunta a gabashi da Tsakiyar Afirka.

A India, kasar da ta fi yawan jama'a yanzu a duniya, mutum daya ne ke amfani da soshiyal midiya cikin ko wadanne mutum uku.

Kazalika an samu karuwa na dadewar da mutane ke yi suna amfani da soshiyal midiya, da minti biyu inda ake yin awa 2 da minti 26 kowacce rana a tsaka-tsaki ke nan.

A nan ma, akwai babban bambanci a tsakanin kasashe, inda 'yan kasar Brazil kan kwashe awa 3 da minti 49 suna amfani da soshiyal midiya ko wacce rana yayin da 'yan kasar Japan suke yin kasa da awa daya.

Shafukan soshiyal midiya da suka fi farin-jini

Kiyasi ya nuna cewa tsaka-tsakin masu amfani da soshiyal midiya suna da shafuka bakwai.

Kamfanin Meta yana da manhaja uku da aka fi amfani da su wato WhatsApp, Instagram da Facebook.

China tana da manhaja uku, WeChat, TikTok da kuma Douyin wanda ake amfani da shi a cikin kasar.

A cewar Kepios, har yanzu Facebook ya fi farin-jini, inda kusan mutum biliyan uku suke amfani da shi duk wata.

YouTube ne na biyu inda mutum biliyan 2.5 suke amfani da shi.

WhatsApp da Instagram su ne a mataki na uku da na hudu, inda mutum biliyan biyu ke amfani da kowannensu duk wata.

TRT Afrika da abokan hulda