Shafukan Meta Facebook da Instagram sun sami tangarɗa sosai a yammacin ranar Talata, inda masu amfani da shafukan da dama suka kasa shiga.
Idan mutane suka yi ƙoƙarin shiga Facebook sai su ga an rubuta: "Ba za ku iya shiga ba, akwai matsala."
Duk ci ga ba da ƙoƙarin shiga ya ci tura.
A Instagram kuwa masu son shiga sukan ga saƙo kamar haka: "Ba za ku iya sabuntawa ba, kuma ba za ku iya shiga cikin asusunku ba.
WhatsApp na aiki
Haka ma masu amfani da shafin Thread wanda shi ma mallakin Meta sun ce ya daina aiki.
Tuni maudu'in "Facebook Down"ya fara tashe a shafin X a ranar Talata da yamman.
Sai dai kuma dandalin Whatsapp wanda shi ma mallakin Meta ne bai samu wata matsala ba kamar sauran.
Har yanzu Meta bai fitar da wata sanarwa kan abin d aya jawo matsalar ba a lokacin wallafa labarin nan.
Yawan mabiya
Facebook shi ne shafin sada zumunta da ya fi kowane yawan mabiya a duniya, inda aƙalla mutum biliyan uku da miliyan 300 ke amfani da shi duk wata.
Instagram, wanda shi ne shafin sada zumunta na huɗu mafi yawan mabiya, yana da mutum biliyan 2.4 masu amfani da shi a duk wata.