Kamfanin Meta ya sanar da ɗage takunkuman da ya saka kan shafukan Facebook da Instagram na ɗan takarar Shugaban Amurka Donald Trump, wanda hakan ya kawo ƙarshen matakin da kamfanin ya ɗauka a kan tsohon shugaban ƙasar bayan magoya bayansa sun afka Majalisar Dokokin Amurka a 2021.
“Tsohon shugaban ƙasar, a matsayinsa na ɗan takarar Jam’iyyar Republcian, ba zai ci gaba da zama a ƙarƙashin hukuncin dakatarwa ba,” kamar yadda Meta ya bayyana a ranar Juma’a.
An dakatar da shafukan Facebook da Instagram na Trump har illa Masha Allahu bayan magoya bayansa sun afka Majalisar Dokokin Amurka a ranar 6 ga watan Janairun 2021, inda aka ga yana bai wa waɗanda suka afkan goyon baya a shafukansa na sada zumunta.
An mayar masa da shafinsa a cikin Fabrairun 2023 amma tare da barazanar ɗaukar mataki a kansa idan ya sake karya doka a nan gaba – wanda wannan shi ne ƙarin takunkumin da Meta ya cire a ranar Juma’a.
“A cikin tsarinmu na bayar da damar faɗin albarkacin baki ta ɓangaren siyasa, mun yi amanna cewa ya kamata jama'ar Amurka su ji ta bakin wadanda aka zaba a matsayin ‘yan takarar shugabancin ƙasa,” kamar yadda Meta ɗin ya rubuta.
Truth Social
Trump, wanda shi ne tsohon shugaban Amurka na farko da aka taɓa kamawa da laifi, kamfanonin Twitter da YouTube su ma duk sun saka masa takunkumi.
Duk da cewa an ɗage masa waɗannan takunkuman a bara, Trump a halin yanzu ya fi isar da saƙo a shafinsa na Truth Social wanda ya ƙirƙira.
Shafinsa na Facebook, wanda ke da mabiya miliyan 34, na da saƙonni waɗanda asalinsu an wallafa su ne a shafinsa na Truth Social, da kuma gayyatar zuwa yaƙin neman zaɓe da kuma bidiyoyi na kamfe ɗinsa.