A shekarar 1975 aka dakatar da aikin ma’aikatar, amma har yanzu hasbara na cikin dabarun da Isra’ila ke amfani da su a duk lokacin da take tsaka yaki-kamar a shekarar 1982 da ta yi mamayar Lebanon, da tashin hankalin intifada na farko a shekarar 1987, da kuma na biyu a shekarar 2000.
A shekarar 2009, bayan hare-haren da ta kai a Gaza da ake kira da “Operation Cast Lead,” sai aka farfado da ma’aikatar a matsayin Ma’aikatar Harkokin ’Yan Kasashen Waje.
Yanzu haka Hasbara ta kara karfi sosai a duniya, watakila saboda ita kanta Fafutikar Kafa Kasar Yahudawa Zallar tana da karfi a sama da kasashen duniya 30.
Farfagandar bayan fage
Cigaban hasbara na na cikin muhimman abubuwan da suke gaban kungiyoyi masu goyon bayan fafutikar Kafa Kasar Yahudu Zalla, wanda doriya ne a kan harkokin tsohuwar Ma’aikatar Hasbara da Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje. Daga cikin wadannan kungiyoyin akwai na gwamnati da masu zaman kansu da kuma na kwararru da sauransu.
Wani wajen da ake yi amfani da shi domin tsara fadada hasbara a duniya shi ne taron duniya domin yaki da nuna wa Yahudawa wariya wato Global Forum for Combating Antisemitism-kungiyar da aka kafa a shekarar 2000 da take shirya taruka lokaci bayan lokacin a Isra’ila da wasu kasashen.
A taron na shekarar 2009, kwamitin kungiyar na, “ Tabbatar da ’yancin Isra’ila: sun bayyana cewa, akwai bukatar “yaki” da ‘kauracewa, rage zuba jari da takunkumi” da ake kakaba wa Isra’ila a fakaice da kuma wasa da tunanin mutane.
Daga cikin hanyoyin da za su bi akwai, “kula na bai-daya” ta hanyar amfani da abin da suka kira da “war room” wato dakin yaki, wanda aka fara assasawa a Jami’ar Reichman da ke Herzliya, wanda ita kadai ce jami’a mai zaman kanta a kasar (inda a da ake kira Cibiyar Ladabi na cikin gida wato Inter Disciplinary Center)
An assasa dakin yakin ne bayan yakin Lebanon na shekarar 2006, kuma aka fara amfani da shi a mamayar Operation Cast Lead a Disamban 2008 ta hanyar hadin gwiwa da jami’ar, da Ma’aikatar Harkokiin Wajen Kasar da kungiyar StandWithUs wadda Gwamnatin Isra’ila ke daukar nauyi.
Amma an tsara yadda gwamnatin za ta cigaba da daukar nauyin harkokin hasbara ta karkashin kasa, a matsayin wata fafutikar mai zaman kanta, wadda babu hannun gwamnati a ciki, duk da cewa ba haka ba ne.
“Ba za mu manta da amfani da kafafen sadarwa na zamani ba wajen yaki da takunkumi da kauracewar da ake wa Isra’ila. Dole mu yi yakin ta bayan fage-Ta hanyar karfafa gwiwar dalibai su yi amfani da fasaharsu da kafofin sadarwarsu wajen fafutikar.”
Haka kuma kwamitin ya kara da cewa, “dole fafutikar ta zama an yi amfani da basira da fasahar Karni na 21 domin nuna wa duniya Isra’ila ta daban.”
Daga cikin hanyoyin cimma wannan manufar, akwai tallata hotunan kyawawan mata, a yada su a kafofin sada zumunta, wanda aka fara da umarnin Ofishin Jakadancin Isra’ila da ke New York.
‘Mujallar nuna tsiraici’ na hotunan matan sojoji
Gwajin farko-farko da aka yi shi ne a shekarar 2007, inda aka yada hotunan matan sojojin Rundunar Tsaron Isra’ila wato IDF wanda ya kunshi wasu kyawawan sojoji mata guda hudu a mujallar maza ta Maxim.
Yada hotunan ya samu goyon bayan Ofishin Jakadancin Isra’ila da ke New York, sannan kungiyar hadakar Amurka da Isra’ila wato American-Israel Frindship League da Israel21c ne suka biya wani bangare na kudin tallata hotunan, kuma wadannan kungiyoyin dukansu suna goyon bayan Isra’ila ne, sannan Gidauniyar Kafa Kasar Yahudawa Zalla ce ke daukar nauyinsu.
An bayyana hotunan a Maxin da cewa: “wadannan kyawawan matan za su iya daukar bindigar Uzi. Shin sojoji matan Isra’ila ne suka kyau a cikin sojoji mata na duniya?” sojoji matan hudu ne a hoton, sannan sunansu iyayensu kawai aka rubuta.
Yarden ta ce, “Harbi ne abin da na fi kauna,” inji ta, inda ta kara da cewa, “ina kaunar harba bindigar M-16, sannan ina da kwarewar yawan dacewa da inda nake hari,” sannan daga baya ta koma rundunar Aman, sashen leken asirin Rundunar Sojin Isra’ila.
Ita kuma Nivit ta ce, “Ni jami’ar leken asiri ce….. ba zan bayyana komai ba, kawai dai na dan koyi harshen Larabci!”
Ta ukun ita ce Gal: “Ina koyar da motsa jiki… sojoji sona domin ina taimakonsu wajen gina jikinsu da lafiyarsu.” Ana kiran Gal da “Tsohuwar Gwarzuwar Kyau ta Isra’ila. Ita ce Gal Gadot, wadda yanzu ta zama jarumar fim, kuma fitacciyar mai fafutikar Kafa Kasar Yahudawa Zalla.
A lokacin, Isra’ila ta yi farin cikin abin da aka yi, inda har Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar ta shirya liyafa ta musamman domin mujallar, wanda Gal Gadot ta halarta.
Gadot ta samu daukaka, har ta kai manyan kamfanin kayayykin irin su Gucci, da Revlon da Reebok sun dauke ta aiki. A shekarar 2016, ta fito a fim din Amurka mai suna Wonder Woman.
Wani ya bayyana cewa, “Ina bakin cikin wadda nake matukar kauna tun ina karami, yanzu ta shiga cikin zaluncin da ake wa Falasdinawa.”
BBC ta ruwaito David Dorfman, wanda a lokacin mai ba da shawara ne a kan harkokin watsa labarai a Ofishin Jakadancin Isra’ila da New York, yana cewa, “Mun lura maza masu karfi a jiki suna daina damuwa da batun Isra’ila, wannan ya sa muka yanke shawarar fito da salon da za mu ja hankalinsu.”
“Isra’ila na son nuna wa duniya cewa ita kasa ce mai matukar son shakatawa, maimakon nuna cewa kasa ce ta addini.”
Wani misali a nan shi ne a shekarar 2016, Mujallar VICE ya wallafa wasu hotuna, wanda kuma sai da ta samu sahalewar Rundunar Tsaron Isra’ila, inda ta akwai wasu hotunan da wani tsohon sojan Isra’ila ya dauka, wadanda ta bayyana da “hotunan kusanci” da ke nuna sojojin kamar maza.
Amfani da kafofin sadarwa na zamani
Wata dabarar hasbara din ita ce amfani da kafofin sadarwa na Rundunar Tsaron Isra’ila, wanda aka kaddamar a shekarar 2007 a kafofin MySpace da Facebook.
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa David Saranga ne ya assasa dabarar, wanda a lokacin shi ne mai ba da shawara kan harkokin watsa labarai na Ofishin Jakadancin Isra’ila a Amurka.
Yanzu Saranga ne shugaban sashin intanent na Ma’aikatar Harkokin Wajen Isra’ila da ke Tel Aviv.
Daga wannan kuma sai YouTube a shekarar 2008, “inda suka fara nuna faye-fayen bidiyon harin jiragen samansua tashoshinsu na YouTube.” Daga baya, sai Rundunar Tsaron Isra’ilar ta fadada zuwa sauran kafofin sadarwa irin su Flickr da Instagram da TikTok.
Rundunar ta bude shafin Flickr a shekarar 2010. Daga cikin hotunan da ta wallafa akwai na “Sojoji mata na Rundunar Tsaron Isra’ila.” wanda aka yi a shekarar 2018, aka sa hotunan matan sanya da kayan soja.
An bude shafin Instagram na rundunar ne a shekarar 2012. Yanzu shafin na da mabiya miliyan 1.3. a shekarar 2016, an samu labarin cewa, “Wani shafin Instagram da ke wallafa hotunan sojoji mata na Israa’ila suna bayyana sashin jikinsu na jan hankalin dubban mabiya.”
Sunan shafin, “Hot Israeli Army Girls,” kuma ya karade kananan mujallin Birtaniya, inda ake nuna kyawawan hotunan matan. Yanzu shafin ba ya aiki, amma tuni rundunar ta koma Twitter da sunan @IDFSpokespercon wanda aka bude a Oktoban 2018.
Shafin TikTok na rundunar da aka bude a shekarar 2020, a 2021 ya samu mabiya 90,000. A yanzu yana da mabiya 373,300.
A shekarar 2021, Mujallar Rolling Stone ta yi rahoto a kan yadda rundunar ta IDF ke amfani da TikTok wajen wallafa hotuna masu nuna tsiraici.
Ita ma Alainna Liloia ta rubuta a shekarar cewa, :”Isra’ila ta fi amfani da farfaganda wallafa hotunan kyawawan mata sojoji a kafofin sadarwa domin kawar da hankalin mutane daga ta’addacin da suke aikatawa a Falasdinu.”
Ma’aikatar Tsare-tsare
Hasbara da kuma fafutikar yaki da wariya da takunkumin da ake nuna wa Isra’ila ne babban aikin Ma’aikatar Tsare-tsare da aka assasa a shekarar 2015.
Darakta Janar na ma’aikatar, wanda tsohon jami’in leken asiri ne ya fito karara ya bayyana cewa suna aiki ne ta karkashin kasa.
Gilad Erdan- wani na kusa da Firayminista Benjamin Netanyahu- ne a lokacin Ministan Ma’aikatar sannan kuma Ministan Tsaron Jama’a.
A shekarar 2017, Erdan ya bayyana dalilin da ya sa ma’aikatar take aiki a boye: “Yawancin ayyukan ma’aikatar da wasu kungiyoyin duniya wadanda ba za su bayyana alakarsu da kasar ba take amfani.”
Amma duk da haka, wani babban tsarin ma’aikata ya fito fili, lokacin da shi Erdan ya yi yunkuyin yada wata manhaja mai suna Act.il, wadda a ciki ake iya wallafa kalaman batsa.
Wani bincike da aka yi, ya bayyana cewa manhajar na da masu aikin sa kai guda 15,000 daga kasashen duniya 73. Akwai kuma wani mai suna 4IL. Erdan da kan shi ne ya kaddamar da manhajar a wani biki da aka yi a New York a shekarar 2017.
A wajen ne aka nuna shi yana daukar hoto da tsohuwar Sarauniyar Kyau ta Isra’ila Yityish “Titi” Aynaw. Har yanzu wannan bidiyon, wanda ake gani a matsayin abin kunyar na nan a YouTube.
Watakila bayanin da za su iya yi a nan shi ne ai dama an fi so dabarar hasbarar ta zama ta bayan fage.
Amma duk da hakan, bayan kafar Electronic Intifada da wasu jaridun sun fallasa ayyukan Act.Il, sun dauki matakin kare kansu ta hanyar nisanta Gwamnatin Isra’ila da manhajar.
Wani shafin intanet na ma’aikatar da aka kaddamar a shekarar 2017 mai suna 4IL- ya nuna harkokin Act’IL.
Da farko da ka shiga za ka ci karo da tambarin ma’aikatar a shafin farko a sama, amma daga baya sai aka mayar da shi can kasa, wanda hakan ya sa kafar Electronic Intifada ta ce an yi haka ne domin, “nisanar da shi daga idon mutane. Sannan kuma duk inda aka ambaci Act.IL aka bi aka cire shi daga manhajar.
Daga cikin manyan dalilan bude wadannan shafukan shi ne nuna hotunan da daga darajar Isra’ila zuwa matsayin da ba kai ba.
Wasu daga cikin sababbin ka’idojin da aka saka wa kungiyiyon masu goyon bayan Isra’ila sun kunshi kauce wa duk wani abu da zai jawo a fara tattaunawa a game da yakin da kasar ke yi, maimakon haka, su dage wajen wallafa hotunan wadanda aka kama ake tsare da su da na rundunar IDF.
Sannan an bukaci hotunan IDF da ake wallafa su zama suna yin daidai da hankali.”
Dole kowane hoto na da sako
Isra’ila ta fahimci cewa mutane suna kaunar hotuna, kuma suna sa mutane su shiga tunani. Ko dai tunani mai kyau, ko kuma marasa kyau.
Misali hoton wajen shakatawa kamar na gabar teku, zai sa mutum ya samu kwanciyar hankali da natsuwa. Amma a dayan bangaren kuma, hoton hatsari, jefa tsoro ne da bakin zai yi a zukatan mutane.
Wani masanin falfasa na Faransa mai suna Roland Barthes ya bayyana hakan shi ma, inda ya ce, “hoto dan rigima ne, ba wai sai dole ya nuna rigimar ba, a’a, saboda a kowane a lokuta da dama, yakan janye mafi yawan ganin mutum da karfi da yaji.”
Hotuna suna daukar mafi yawa daga cikin abubuwan da mutum yake iya tunawa. La’akari da abin da hoton ke nunawa, kowa yana da yadda zai ji bayan ya kalla. Kuma ko da mun kawar da idanunmu bayan kallon, dole akwai ragowar abin da muka gani da za mu dade muna tunaninsu.
Ganin cewa hotunan suna aika sako, shi ya sa ba abin mamaki ba ne ganin Isra’ila na amfani da su domin wata mummunar manufa. Abin takaicin ma shi ne yadda ake bayyana tsiracin mata a hotunan domin a ja hankalin mutane su goyi bayan rundunar ta IDF.
A takaice dai tana amfani da hotunan wajen jawo hankalin mutane zuwa ga rundunar tsaron. Wannan kuma yana da alaka da kyawun jikin matan, wadanda a hotunan suke jan hankalin mutane da jikinsu.
Ta hanyar amfani da wannan dabarar, Isra’ila ta yaudari mutane cewa rundunar tsaron IDF ba azzaluma ba ce saboda wadannan matan da suke nunawa, wanda kuma kyauwunsu ne ake kallo.
Sai dai ana ganin akasin hakan a yanzu daga hotunan Gaza da ake gani na yanzu, wadanda yawancin mutanen Gaza da kansu ne suka fito da su-hotuna da bidiyoyi- wadanda suke fallasa ta’addacin rundunar IDF a kan Falasdinawa.
Wadannan hotunan sun sa mun ga zahirin abin da ke faruwa, maimakon hotunan ’yan matan da suke nuna wa mutane. Haka kuma hotunan Gaza na kara bayyana bukatar da ke akwai na fadada tunani a kan abubuwan da ake nuna mana.
Wata marubuciyar Amurka, Susan Sontag ma ta bayyana hakan, inda ta ce, “Hotunan (na wahala da kunci) sun ba su wuce a yi amfani da wajen mayar da hankali ba, a yi tunani, sannan a bibiyi wahalar da mutane suke ciki, wanda kuma kasa mai karfi ce ta jefa su,” in ji ta.
“Wane ne ya jawo abin da muke gani a hotunan? Laifin wane ne” shin za a iya kare aukuwar hakan? shin akwai wasu ayyukan wata kasa da ya kamata a kalubalanta, amma ba mu yi ba? Dukka wadannan na bukatar fahimta na tsanaki.”
Duk da cewa Sontag ta yi gaskiya cewa hotunan wahalhalu kadai ba za su tilasta daukar mataki ba, sai dai ai kamar yadda ta bayyana, ba su da kyawun gani.
Idan aka lura da yadda hotunan suke, akwai bukatar a kalubalanci abin da ake nuna mana. Wannan na da matukar muhimmanci domin daukar mataki na gaba.
Yanzu ana amfani da dabaru da dama yanzu a duniya, inda mutane da dama suke ta zanga-zangar a tituna da wasu wuraren domin nuna goyon bayansu ga Faladinawa da kuma nuna rashin jin dadin wahala da kuncin da Isra’ila ta jefa su.
Amma ba kamar yadda masu amfani da kafofin sadarwar suke yi ba, masu zanga-zangar suna bayyana ta’addanci da rashin adalcin da Rundunar IDF din take yi ne, sannan suke kira a tsagaita haka.
Wannan watakila ba zai ja hankali ba saboda ba hotuna “masu zafi” ba ne kamar na masu amfani da kafofin sadarwar, amma yana nuna wani abun mai muhimmanci daga bangaren masu zanga-zangar: juriya da karfin gwiwar nuna wa Isra’ila yatsa.
Hotunan da suke fitowa daga Gaza ma za su kara fusata masu zanga-zangar, wadanda ke kara nuna yadda cigaba da hare-haren Isra’ila a kan Falasdinawa ke barazana da zaman lafiyar duniya.
Masu amfani da sada zumunta
Masu amfani da kafofin sadarwana suna wallafa hotunansu ne masu kyau tare da abin da suke tallatawa, watakila da wani dan rubutu, amma ba dukkansu ba ne suke fitowa a fili suna goyon bayan ta’addancin da ake yi ga wata al’umma ba.
Idan ka dauki tsarin, ka hada sababbin dabarun yaki na zamani, za ka alamar tsarin da IDF ke bi, kamar yadda Natalia Fadeev, wadda ta fi shahara a kafofin sadarwa da sunan Gun Waifu kamar ke yi a Facebook da YouTube da X (Twitter a da) da Instagram.
Ba Fadeev kadai ba ce, akwai sauran mata irin su Orin Julie mai fafutikar rike bindiga da kare hakkin mata da koyar da harbi kamar yadda shafinta na LinkedIn ya nuna.
Hada amfani da kafofin sadarwa da aikin sojin Isra’ila ba sabon abu ba ne, sai dai ganin yadda ake samun sababbin hotuna da bidiyoyin da suke fitowa daga Gaza, yanzu Isra’ila ta kara kaimi a kafofin sadarwa don cigaba da mamaye kafofin.
Ko dai suna da alaka da sojijin ko a’a, wadanan hotunan ana wallafa su ne domin a dauke hankalin wadanda ba su da alaka da yakin daga asalin abin da ke faruwa, kamar yadda Dokta Jessica Maddox, mataimakiyar farfesa a tsangayar koyon aikin jarida ta Jami’ar Alabama ta bayyana.
“Wata dabara ce ta dauke hankalin mutane da kara samun magoya baya- ko dai dauke hankali daga bakin ciki da damuwar kallon yaki, ko kuma mamakin yadda sojojin suke da kyau,” in ji Maddox.
Yanzu da ’yan jarida da ke Gaza suke kara fallasa asalin abubuwan da suke wakana, da kuma yadda kafofin watsa labarai na duniya suke cigaba da boye gaskiyar lamarin, shafukan kafofin sadarwar magoya bayan Isra’ila a TikTok da Instagram suna cigaba da yada abubuwa da burin boye ainihin abin da ke faruwa.
Yanzu kasashe sun gane amfani da amfani da kafafen sadarwa wajen sauya tunanin mutane. Misalin hakan shi ne yadda Rasha ta yi amfani kafofin wajen boye asalin abin da ke faruwa a Ukraine.
Maddox ta bayyana wa TRT cewa, “Ana yin haka domin a nuna wa duniya cewa kasar da ake magana a kanta din ba muguwa ba ce.”
Ta kara da cewa, “Kasashen da suke amfani da masu amfani da kafofin sadarwa, suna yi ne domin nuna cewa suna kula da hakkin ‘yan Adam.
“Abin da nake nufi shi ne, kasashen da suke amfani da kafofin sadarwa suna haka ne domin farfaganda, suna nuna kasar ko sojojinta a matsayin abar sha’awa. Burin masu amfani da kafofin sadarwa shi ne jan hankali, don haka ita ma farfaganda sojojin a kafofin sadarwa hakan take,” in ji ta.
Wannan dabarar ba IDF kadai ke amfani da ita ba. Masu amfani da kafafen sadarwa da suke zaune a inda ake yaki da ma masu alaka da sojoji suna amfani da ‘manhajoji ko shafukan intanet” domin nuna abin da ke faruwa.
A bangaren wallafa abubuwan da suke da alaka da kafa Kasar Yahudawa Zalla misali, ana yin hakan ne ta hanyar tura wasu sakonnin da suke nuna cewa batun kashe-kashen da ake zargin Isra’ila da su akwai Karin gishiri a miya.
Sai dai Maddox ta ce yana da kyau a fahimci abubuwan da ake nunawa, “tsararru, kuma ra’ayin wani bangare ne,” sannan, “fahimtar bambancin karfin da ke tsakanin kasar da aka danne, da mai danniyar na da muhimmanci.”
“Masu amfanin da kafofin sadarwa da ba su da alaka da rundunar IDF za su iya bayyana rashin jin dadinsu ga Gwanatin Isra’ila, amma ko a cikinsu din, da yawa goyon baya suke.”
Don haka yaya dabarar Isra’ila ke aiki a kafofin sadarwa wajen nuna abin da ke faruwa da samun goyon baya?
Daga wulakanta cin fuskar Falasdinawan ta hanyar sa wakokin yara suna nuna kamar an kama su, ko kuma an rufe musu idansunsu, da mayar da ta’addancin da ake wa mutanen Gaza abin dariya alhalin suna cikin kunci da sauransu, babbar illar da aka yi wa Isra’ila wajen bata sunanta a kafofin sadarwar daga ita kanta Isra’ilar ce da rundunar IDF din.
Mutane da dama sun fara dawowa daga rakiyar bayanan da suke fitowa na wulakanta Falasdinawa da kuma nuna goyon baya ko bayyana dalilin Gwamnatin Firayminstan Isra’ila Banjemin Netanyahu na wannan ta’asar da take aikatawa, wadda aka kashe sama da Falasdinawa 22,000, aka kuma jikkata akalla 57,035.
Yadda lamarin yake a kafofin sadarwa, a cewar Maddox shi ne, mutane, musamman matasa, “sun fi goyon bayan Falasdinawa.”
“Wannan ya sa dole TikTok ta fito ta bayyana cewa ba ya nuna kiyayya ga Isra’ila,” inji ta, sannan ta kara da cewa,”matasan suna matukar goyon bayan Falasdinawa.”
Kamar yadda Maddox ta bayyana, “duk da cewa wannan dabarar ta amfani da kafofin sadarwa na amfani ga wasu, al’amarin na ya fi karfin a bayyana shi a rubutun da bai wuce kalma 280 ba, ko kuma bidiyon dakika 60 kawai.”