Sau wajen bakwai Momika yana kona Kur'ani a wurare daban-daban a Sweden daga watan Janairu zuwa Agusta. Hoto: AA

TikTok ya toshe shafin Salwan Momika, wanda ya kona Alkur'ani sau wajen bakwai a Sweden, daga samun kudi ta kafar.

Jami'an TikTok sun tabbatar da cewa an toshe hanyar da masu amfani da kafar za su dinga bai wa Momika kudi, kamar yadda Gidan Rediyon Sweden ya ruwaito a ranar Talata.

Daga yanzu, masu amfani da shafin Tikotok ba za su iya bai wa Momika "kyaututtuka ba", a yayin da Momika ya wallafa bidiyo a shafin.

Momika shi ne mutumin da kona Alkur'ani Mai Tsarki sau wajen bakwai a wasu jerin zanga-zangar adawa da Musulunci da yake yi, lamarin da ya jawo tashin hankali a kasashen Musulmai.

Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Sweden, TT, Momika, wanda ke zaune a birnin Stockholm ya ce miliyoyin mutane ne suka kalli bidiyoyin da ya wallafa na kona Kur'ani a Tiktok.

Ya ce ya samu daga tsakanin dala 100 zuwa dala 300 daga Tiktok a cikin awa daya lokacin da yake watsa bidiyon kai tsaye, sannan kuma ya ce a yanzu ba shi da wata hanyar samun kudi bayan da Tiktok ta toshe masa waccar hanyar samun kudin.

Jaridar Aftonbladet ta ruwaito cewa an kama Momika da laifi a shekarar 2021 kan yi wa wani dan kasar Eritrea mai neman mafaka barazana da wuka.

Jaridar ta kara da cewa an daure Momika tsawon awa 80 tare da yin aikin da ba za a biya shi ba, kuma an umarce shi da ya biya tarar dala 1,000 a matsayin diyya ga dan Eritriyan da ke neman mafakar.

A hannu guda kuma, wani fitaccen kwararre kan miyagun laifuka ya bayar da shawarar cewa a dinga daure duk wadanda suke amfani da 'yancin fadin albarkacin baki suna kona Kur'ani.

'Yancin fadin albarkacin baki ba abin da "wasu fitinannun mutane kalilan" za su dinga amfani da shi ba ne sakaka wajen yi wa burikan kasar Sweden da kuma rayukan 'yan kasar barazana ba, kamar yadda Leif Persson ya shaida wa wani gidan talabijin na kasar TV4.

Persson ya kara da cewa yana ganin bai kamata a kyale Momika da dan siyasar nan dan kasar Sweden da Denmark wato Rasmus Paludan, ko sauran mutane irin su su dinga wulkanta Kur'ani ba irin haka.

Neman tsokana a Sweden da Denmark

Sweden da Denmark sun sha caccaka saboda barin mutane suna kona Kur'ani a bainar jama'a karkashin kariyar 'yan sanda.

Paludan na ci gaba da kona Kur'ani a biranen Malmo da Norrkoping da kuma Jonkoping na Sweden da ma babban birnin kasar Stockholm, a yayin hutun Easter na bara.

A ranar 21 ga watan Janairu ne ya kona Kur'ani a gaban Ofishin Jakadancin Turkiyya da ke Sweden, sannan ranar 27 ga Janairun ya sake yin hakan a gaban ofishin jakadancin Turkiyyan a Denmark.

Momika ya sake kona Kur'ani a gaban wani masallaci a Stockholm ranar 28 ga watan Yuni, ranar Babbar Sallah.

Sannan a ranar 20 ga watan Yuli a gaban ofishin jakadancin Iraki da ke Sweden ya yi jifa da Kur'ani da tutar ksar Iraki a kasa ya tattaka su. Sannan ranar 31 ga watan Yuli ya sake kona Kur'ani a gaban majalisar dokokin Sweden.

Bahrami Marjan ma ya yi irin wannan tsokanar a gabar tekun Ängbybadet a Stockholm ranar 3 ga watan Agusta.

A farkon watan Agusta Momika ya sake kona Kur'ani a gaban ofishin jakadancin Iran a Stockholm.

Sannan tsokana ta baya-bayan nan da ya yi ita ce wacce ya kona Alkur'ani a gaban wani masallaci a Stockholm a ranar Alhamis din da ta gabata.

AA