Jirage marasa matuƙa na ta shawagi a sararin samaniya sannan gwanayen harbi daga ɓoye suna ta sa ido a yayin da miliyoyin Amurkawa suka kaɗa ƙuri'unsu a ranar Talata a zaɓen Amurka da ya fi kowanne jawo arrabuwar kawuna a tarihi.
Mataimakiyra Shugaban Ƙasa Kamala Harris da ɗan takarar Jam'iyyar Republican Donald Trump suna fafatawa a zaɓen wanda ke matuƙar jan hankali.
Idan Trump ya yi nasara zai zamo shugaban ƙasa na farko da aka taɓa tuhuma da aikata manyan laifuka.
Trump zai kuma zamo shugaban ƙasa na biyu a tarihi da zai yi wa'adai biyu ba a jere ba a matsayin shugaban ƙasa, bayan Grover Cleveland a ƙarshen ƙrni na 19.
Ita kuwa Haris tana fatan zama mace ta farko, kuma mace baƙar fata ta farko, sannan 'yar asalin yankin Asiya ta farko da za ta shiga Fadar White House.
Jami'ai sun samar da matakan tsaro a rumfunan zabe a fadin ƙasar a ƙoƙarinsu na tabbatar da cewa komai ya gudana cikin aminci.
Don ƙara ƙarfafa tsaro, an girke 'yan sanda da dama a kan tituna a faɗin ƙasar.
1329 GMT — Ana ta ɗaukar matakai a Washington kan yiwuwar ɓarkewar rikici a zaɓen Amurka
Ana ta rufe harkokin kasuwanci a yankunan da ke kusa da Fadar White House stare da ɗaukar matakan tsaro yayin da ake taka tsantsan cikin fargabar ɓrkewar rikici a ranar zaben - da kuma kwanaki masu zuwa.
Magajin Garin DC Muriel Bowser ya ce hukumar 'yan sanda tana kuma ƙara ƙaimi a gundumomin kasuwanci da ke dukkan yankuna takwas na birnin.
Shugabar 'yan sandan birnin Pamela Smith a wani taron manema labarai ta kuma tabbatar wa mazauna birnin cewa sashenta ya shirya don tunkarar duk wani abu da ranar zabe za ta iya kawowa.
Ta ce, "Tawagarmu ta kasance da cikakkiyar himma da kuma taka tsantsan," in ji ta. "Mu ne mafi ƙwarewa a kasar nan kan abin da muke yi, kuma za mu ci gaba da aiki ba dare ba rana don kiyaye Washington DC, da kuma kiyaye mazaunanmu."