Sabbin hare-haren Isra'ila sun kashe mutum 26 a kudancin Lebanon / Hoto: AA

Litinin, 18 ga watan Nuwamba, 2024

0842 GMT –– Aƙalla mutum 26 ne suka mutu sannan gommai suka jikkata bayan da Isra'ila ya ƙddamar da wasu sabbin hare-haren sama a kudancin Lebanin, in ji kafar yaɗa labarai ta ƙasar.

Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hare-haren sama 10 a birnin Nabatieh, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum takwas tare da jikata wasu da dama, in ji kamfanin dillancin labaran NNA.

Sannan an kashe wasu ma'aikatan lafiya shida a wani harin sama da aka kai Hukumar Lafiya ta Musuluncin a garin Arab Salim.

Kazalika wani mutum ɗayan ya sake rasa ransa a harin da aka kai gundumar Bent Jbeil, a cewar NNA.

Jiragen yaƙin Isra'ila sun kuma ƙaddamar da hare-hare da dama a yankunan da ke kusa da Tyre, lamarin da ya kashe mutum 11 tare da jikkata 48, in ji kamfanin dillancin labaran.

0549 GMT –– Harin da Isra'ila ta kai a yankin Mawasi na Gaza ya kashe mutun 4 'yan gida ɗaya

Kamfanin dillancin labaran Falasɗinawa WAFA ya ruwaito cewa Isra'ila ta kashe mutane da dama, ciki har da yara, a harin bama-bamai da ta kai da sanyin safiya a kudancin Gaza.

Majiyoyi daga asibiti sun ce dakarun Isra'ila sun kashe mutum huɗu 'yan gida ɗaya –– wani mutum da matarsa da 'ya'yansa. 'Yarsu ta tsallake rijiya da baya amma ta samu raunuka masu muni, sakamakon luguden wutar da sojojin Isra'ila suka yi a wani tanti da 'yan gudun hijira suke samun mafaka a yankin Al Mawasi da ke yammacin Khan Younis.

Isra'ila na ci gaba da luguden wuta a yankin Al Mawasi na Gazaduk da cewa Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana shi a matsayin "tudun-mun-tsira."

Mazauna yankin sun ce Isra'ila ta sha kai musu hari babu ƙaƙƙautawa.

Ƙarin labarai👇

0633 GMT –– 'Wani abin fashewa' ya faɗa kudancin Jordan ba tare da jikkata kowa ba: Rundunar sojin Jordan

Rundunar sojin Jordan ta ce "wani abin fashewa" ya faɗa a yain da ke kan iyaka na lardin Aqaba da ke kudancin Isra'ila.

Wata sanarwa ta ambato majiyoyin soji suna cewa babu wanda ya jikkata sakamakon faɗuwar abin.

Ta ƙara da cewa jami'an tsaro sun isa wurin da lamarin ya faru.

Sai dai sanarwar ba ta faɗi sunan abin da ya faɗa a yankin ba, ko kuma daga inda aka harba shi. Birnin Aqaba yana daura da birnin Eilat na kudancin Isra'ila.

TRT World