A ranar Litinin 18 ga watan Nuwamba ne ake soma taron ƙasashen G20 a birnin Rio de Janeiro na Brazil.
Ana sa ran taron na bana zai mayar da hankali kan yaƙi da talauci da haɓaka samar da kuɗi domin daƙile matsalolin sauyin yanayi.
Wannan ne karo na ƙarshe da Shugaban Amurka Joe Biden zai halarci taron na G20 na ƙasashe 20 mafi ƙarfin tattalin arziki.
Baya ga shugaban Amurka, Shugaban China Xi Jinping da shugabannin Australia da Birtaniya da Masar da Faransa da Jamus da Indiya da Indonesia da Japan duk za su halarci wannan taron.
Shi ma Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu tun a ranar Lahadi ya kama hanyar tafiyar zuwa birnin na Rio de Janeiro domin halartar taron na ƙasashen G20. An kafa ƙungiyar ta G20 ne a shekarar 1999 domin magance matsalolin tattalin arziƙi da duniya ke fama da su.
Za a gudanar da taron ne gidan tarihi na kayayyakin zamani na kimiyya a birnin na Rio de Janerio.
An tsaurara matakan tsaro a wurin taron, wanda ke zuwa kwanaki bayan wani harin bam da aka kai a Kotun Kolin Brazil da ke Brasilia da bai yi nasara ba, wanda ake kyautata zaton wani mai tsatsauran ra’ayi ne yaje wurin domin ƙunar baƙin wake, inda ya kashe kansa.
Kimanin sojoji da 'yan sanda 25,000 ne aka girke a kewayen birnin, ciki har da tashoshin jiragen sama da tashoshin jiragen ruwa, an kuma jibge motoci masu sulke a kewayen wurin da za a gudanar da taron.
Haka kuma aƙalla kemarorin tsaro dubu biyar da ke kan titi za a yi amfani da su wurin sa ido kan gudanar da taron, haka kuma za a yi amfani da jirage marasa matuƙa da jirage masu saukar ungulu waɗanda za su rinƙa sa ido daga sama.
G20 ko kuma G21?
Ƙasashe 19 da kuma Ƙungiyar Tarayyar Turai suka haɗu domin samar da ƙungiyar G20.
Sai dai a shekarar 2023, Firaministan Indiya Narendra Modi yayin taron ya sanar da Ƙunigyar Tarayyar Afirka wato AU a matsayin mamba ta 21 a ƙungiyar ta G20.
Wannan ne karo na farko da ƙungiyar ta AU za ta je taron na G20 a matsayin cikakkiyar mamba.
Sai dai ana ganin akwai buƙatar bayan shigar ƙungiyar ta AU ƙungiyar G20, ya kamata a mayar da sunan ƙungiyar G21.
Shi suna yana da nauyi – yana ƙara armashi da nuna karɓuwa. Rashin sauya sunan zai sa a rinƙa ganin tamkar a nuna wariya ga Afirka ko kuma ba a ɗauke ta da muhimmanci ba, kamar yadda Abhishek G Bhaya ya bayyana, wanda babban edita ne mai sharhi a TRT.
Ya kuma ƙara da cewa Rashin sauya sunan zuwa G20 zai iya ɗaukar wata ma’ana ta daban.
Zai iya nuna cewa ba a ɗaukar Afirka da muhimmanci sosai musamman wurin yanke hukunci ko kuma ɗaukar matakai waɗanda za su kawo sauyi ga tattalin arziƙi, in ji Abhishek.