Simon Ateba ya yi ikirarin cewa an saba wa kundin tsarin mulkin Amurka. / Hoto: AFP

Daya daga cikin 'yan jaridar da ke aiki a fadar White House ya yi karar Sakatariyar Yada Labarai Karine Jean-Pierre a gaban kotu, bayan an ki sabunta shaidarsa ta izinin yin aiki a fadar.

A karar da dan jaridar Kamaru Simon Ateba, wanda yake aiki da Today News Africa, ya shigar ya yi zargin cewa dokokin da fadar White House ta sanya da suka dakatar da takardar izinin aikinsa sun saba wa kundin tsarin mulkin Amurka, kamar yadda rahotanni suka bayyana ranar Litinin.

A ranar 5 ga watan Mayu, fadar White House ta fitar da wasu sabbin dokoki kan izinin aiki a fadar.

Kuma wannan ne karo na farko a tarihin Amurka da aka gindaya wasu sharudda da za a kwace wa 'yan jarida takardar izinin aiki.

Kafafen yada labarai sun soki al'amarin, suna masu cewa fadar White House ta gindaya sabbin dokoki ne saboda hana dan jaridar sabunta takardar izininsa aiki a fadar.

Yanzu sabuwar dokar White House ta bukaci 'yan jarida su rika neman takardar izinin aiki daga Majalisar Dokokin Kasar ko kuma Kotun Kolin Kasar don cika sabbin sharuddan.

Ateba ya ce ba zai iya sabunta izininsa ba saboda ba shi da wasu takardu kuma ya yi zargin cewa an kitsa haka ne saboda shi.

Yayin zantawa da manema labarai a ranar 26 ga watan Yuni, Ateba ya katse lumfashin sakatariyar yada labarai yayin da take magana kuma bai fasa katse sauran 'yan jarida ba yayin da suke magana.

Amma kamar yadda aka bayyana bayan Sakatariyar Yada Labarai Jean-Pierre ta dakatar da Ateba daga yin tambayoyi har tsawon wata tara, ya fara yin ihu da katse mutane idan suna magana don ya yi tambayarsa.

AA