Shugabannin kasashe 10 da kungiyoyin kasa da kasa sun halarci wannan taron. Hoto/AA

Sama da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 20 -- ciki har da Turkiyya- suka amince su kaddamar da wani tsari wanda ake kira “Rome Process” domin dakile ci-rani ba bisa ka’ida ba da safarar bil adama.

Taron kasa da kasa kan raya kasa da ci-rani a ranar Lahadi wanda tsari ne na kasar Italiya, ya karbi bakuncin manyan shugabanni da jami’an diflomasiyya daga kasashen Mediterranean, da kasashen Gabas ta Tsakiya da na yankin Gulf.

Firaiministan Italiya Giorgia Meloni ta karbi bakuncin mahalarta taron inda suka tattauna kan mafita mai dorewa wurin yaki da masu zuwa ci-rani ba kan ka’ida ba da kuma matakan da za a iya dauka wurin dakile ci-rani daga kasashen da ‘yan ci-ranin ke fitowa.

Kasashen da suka halarci taron da kuma kungiyoyin kasa da kasa wadanda suka hada da Asusun Bayar da Lamuni da Bankin Raya Kasashen Musulmi da Bankin Duniya sun amince da aiwatar da tsarin.

Kamar yadda aka aka cimma matsaya a lokacin taron, gwamnatin Italiya ta bayyana cewa tsarin “Rome Process” na da burin magance matsalar daga tushen da ke jawo mutane suna barin muhallansu, da kuma dakile ci-rani ba bisa ka’ida ba da safarar mutane a yankin na Mediterranean da Gabas ta Tsakiya da Afirka.

“Mahalarta taron sun amince su yi aiki tare da juna bisa tsari, da tara kudin da ya kamata da aiwatar da tsaruka na hadin kai da ayyuka ga kasashen da tushen matsalolin suke,” in ji sanarwar.

Domin samun wannan nasara ta hanyar samar da tsari da yin ayyuka, bangarorin za su mayar da hankali wurin ayyukan ci-gaba, da yaki da talauci da samar da ayyukan yi ta hanyar samar da ilimi mai inganci.

Kokarin da samar da mafaka da hanyoyin da za a bi wurin kula da ci-rani da hada kai domin ganin kowa ya sauke nauyin da ya rataya a kansa yadda ya kamata na daga cikin abubuwan da aka tattauna a kai.

Aljeriya da Bahrain da Masar da Habasha da Girka da Jordan da Kuwait da Lebanon da Libya da Malta da Mauritania da Morocco da Nijar da Qatar da Oman da Saudiyya da Sifaniya da Tunisia da Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Greek Cypriot Administration su amince da hada hannu domin daukar mataki.

Tattaunawa tsakanin kasashe da kungiyoyi bisa mutunta juna

A lokacin tattaunawa yayin bude taron, Meloni ta ce abin da suke kaddamarwa a yau shi ne “tattaunawa tsakanin juna, bisa mutunta juna.”

“Tsakanin Turai da yankin Mediterranean, ba za a iya samun dangantaka mai gasa ko rikici ba, saboda a zahiri, bukatu sun fi dacewa fiye da yadda mu kanmu muka gane, "in ji wani rahoto na kamfanin dillancin labaran Italiya ANSA.

Meloni ta kuma ce “Italiya da Turai na bukatar ‘yan ci-rani,” “ba za su iya nuna cewa,” wadanda suka shigo ba bisa ka’ida ba za a kyautata musu.

Ministan harkokin waje na Turkiyya Hakan Fidan na daga cikin wadanda suka halarci taron, inda ya jaddada muhimmancin hadin kan yankuna a lokacin taron wanda aka yi kan dakile ci-rani ba bisa ka’ida ba, lamarin da ya bayyana a matsayin wani kalubale da kasashen Mediterranean ke fuskanta kamar yadda majiyoyin diflomasiyya suka bayyana.

Domin dakatar da tururuwar ‘yan ci-rani tun daga tushe, ministan harkokin waje na Turkiyya ya ce dole ne a dakile matsalolin da suka hada da rikici da tattalin arziki domin cimma wannan burin.

Fidan kuma ya kara jaddada muhimmancin daukar nauyin ‘yan ci-rani da suka tsallaka kasashe ba bisa ka’ida ba, inda ya yi kira ga kasashe da su daina kin jinin baki da koya wa kai juriya domin kare ‘yancin bil adama.

AA