1344 GMT — Ma’aikatan lafiya biyu ne suka mutu yayin da wasu hudu suka jikkata sakamakon wani hari da jiragen yakin Isra'ila suka kai a kudancin kasar Lebanon, lamarin da ke nuni da cewa sojojin na Isra'ila sun kai hari kan ma'aikatan lafiya da ke bakin aiki wadanda ke kokarin ba da agajin gaggawa ga mutanen da suka jikkata da kuma ƙoƙarin kai su asibiti.
Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar inda ta ce akwai ma’aikatan lafiya biyu waɗanda suka ɓata inda a halin yanzu ana ƙoƙarin gano su.
Ma’aikatar ta kuma ce akwai wani ma’aikacin lafiya ɗaya daga Islamic Scout Asscoiation da ke Burj Rahal wanda aka kashe da safiyar Asabar a lokacin da yake ƙoƙarin ceto wani wanda ya jikkata.
1026 GMT — Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza na dab da kaiwa 43000
Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta bayyana cewa aƙalla mutum 43,799 aka kashe a cikin fiye da watanni 13 da aka yi ana yaƙin Gaza a Falasɗinu.
Adadin waɗanda suka rasu ya hada da mutum 35 a sa’o’i 24 da suka gabata, kamar yadda ma’aikatar ta tabbatar, inda ta ce mutum 103,601 suka jikkata tun daga 7 ga watan Oktobar 2023.
2049 GMT — Isra’ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa 11 a ci gaba da kisan ƙare-dangi a Gaza
Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 11 ta jikkata wasu da dama a ruwan bama-bamai da ta yi kudanci da arewacin Gaza, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na WAFA.
Kamfanin dillancin labaran na Falasɗinawa ya ce masu mamaya na Isra’ila sun kashe fararen hula huɗu sun kuma jikkata da dama a hare-haren da suka kai unguwar al-Karama a arewacin Birnin Gaza.
Sojojin na Isra’ila sun kuma kashe wasu mutanen biyu sannan sun jikkata wasu bayan sun jefa bam wani gida a unguwar Zeitoun dake kudu maso gabshin birnin.
Kamfanin dillancin labaran ya ƙara da cewa sojojin Isra’ila sun harbe wani matashi lokacin da yake yunƙurin guduwa daga arewacin Gaza zuwa tsakiyar birnin, don kauce wa yankin da aka killace.
A kudancin Gaza kuwa, masu aikin ceto sun ton gawawwakin wasu fararen hula huɗu da aka kashe a hare-haren Isra’ila ta sama a wurare daban-daban a Rafah.
2202 GMT — Hezbollah ta kai hare-hare kan sansanoni sojojin Isra’ila
Hezbollah ta sanar da kai hare-haren makaman roka da jirage marasa matuka kan sansanonin sojojin Isra’ila, da matsugunai da sojoji a arewacin Isra’ila da kudancin Lebanon.
Kungiyar ta Lebanon ta ce ta kai hare-hare 31 kan sojojin Isra’ila da sansanoninsu da kuma matsugunnensu.
Ta yi da’awar cewa mayakanta sun kai hari kan sansanin sojojin Isra’ila na Tirat Carmel a kudancin Haifa, da sansanin Shraga kusa da Acre, inda suka yi amfani da makaman rokoki da aka bunƙasa su.
Ta kuma ba da rahoton kai hari kan taron sojojin Isra’ila tara a kusa da Doviv da Sa’sa da Misgav da Yorn a arewacin Isra’ila.
Ƙari a kan haka, Hezbollah ta ce ta kai hari kan wuraren sojojin Isra’ila 19 a kusa da garuruwan Maroun al-Ras da Markaba da Khiyam da Hanine da Talloussah a Lebanon.
Gidan rediyon Isra’ila ya ce an gano aƙalla makaman roka 40 da kuma jirage marasa matuka uku waɗanda aka harbo su daga Lebanon zuwa kudancin Isra’ila, abin da ya sa aka kunna jiniyar hare-haren sama a arewacin Isra’ila.