Mai ɗakin Shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta yi bikin Ranar ‘Yancin kan Falasɗinawa da aika wani muhimmin saƙon goyon baya, tana bayyana ta a matsayin wata rana da aka kafa don neman adalci da kuma tuna wa juna irin yadda aka damu da batun kare alfarmar ɗan’adam.
Da take waiwaye kan taken ranar a bara “Zuciya Ɗaya ga Falasɗinu: Taron Matar Shugaban Ƙasa,” ta jaddada kiran da ake yi na tsagaita wuta a Gaza, wanda ya ma wuce batun neman zaman lafiya zuwa adawa da duk wani mataki na keta alfarmar dan’adam da dokokin duniya.
“Mun yi watsi da duk wani tsari da zai raba mutanen da ba su yi laifin komai ba da rayuwarsu, sannan yake jefa rayuwar yara cikin duhu,” a cewar Emine Erdogan a shafin X ranar Juma’a.
Taron ya samu halartar matan shugabannin ƙasashe daga faɗin duniya, ciki har da mai ɗakin shugaban Azerbaijan's Mehriban Aliyeva da mai ɗakin shugaban Brazil Rosangela da Silva.
Mai ɗakin Shugaban na Turkiyya ta nuna matuƙar damuwa kan yaƙin da ake ci gaba da yi, tana bayyana cewa muguntar Isra’ila a yanzu ta zarce Falasdinu ta shiga Lebanon.
Ci gaba da yunƙuri don tabbatar da tsaro
Da take jaddada irin yadda Turkiyya ta damu da batun Falasɗinu, ta yi alƙawarin ci gaba da yunƙurin tabbatar da tsaro da zaman lafiya ga dukkan mutanen da muguntar Isra’ila ke cuzgunawa, musamman ma Falasɗinawa.
“Adalci ba wai abu ne kawai da ya kamata a tabbatar ba, tabbataccen haƙƙine na duka mutanen da ba ruwansu, kuma tsayawa don tabbatar da wannan haƙƙin wani zakaran gwajin dafi ne ga duka yadda muke ɗaukan batun bil’adama, a cewarta.
Emine Erdogan ta kuma miƙa ta’aziyya ga rayukan da aka rasa wajen fafutukar ‘yancin Falasɗinu, ta kuma miƙa jinjina ga waɗanda suke ci gaba da yin tsayuwar daka wajen kare ƙasarsu.
“Ina jinjina ga waɗannan gwarazan da suke kare ƙasarsu, su kuma shahidai Allah ya sa sun huta,” kamar yadda ta faɗa a lokacin da take kammala jawabinta.
A kunnen ƙasahi kan Ƙudirin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya na tsagaita wuta nan take, Isra’ila ta ci gaba da kai munanan hare-hare kan Falasɗinawa a Gaza tun daga 7 ga Oktoban 2023.
Kisan ƙare-dangin na Isra’ila ya raba kusan dukkan jama’ar yankin da mahallansu a daidai lokacin da aka killace yankin, abin da ya janyo mummunan ƙarancin abinci da ruwa da kuma magani.