An jefa abubuwan fashewa guda biyu kusa da gidan Netanyahu a Caesarea

An jefa abubuwan fashewa guda biyu kusa da gidan Netanyahu a Caesarea

‘Yan sanda sun ce Netanyahu da iyalensa ba sa gidan lokacin da lamarin ya faru.
Jami'an tsaron Isra'ila suna tafiya a titin gidan Firaminista Netanyahu a Caesarea. / Hoto: AFP

‘Yan sandan Isra’ila sun ce an jefa wasu abubuwan fashewa wajen gidan Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a Ceasarea, kudancin Isra’ila a ranar Asabar.

“Da misalin 19:30 agogon Tel Aviv (17:30 GMT) an gano wasu abubuwan fashewa guda biyu a kusa da gidan Firaminista a Ceasarea, sun faɗa a harabar wajen,” a cewar sanarwar ‘yan sanda.

Sanarwar ta ƙara da cewa an tura dakaru daga rundunar ‘yan sanda da Hukumar Tsaro ta Shin Bet (Shabak)

Natanyahu da iyalensa ba sa gidan lokacin da lamarin ya faru, a cewar ‘yan sanda.

‘Yan sandan sun ƙara da cewa sun “ƙaddamar da binciken haɗin gwiwa tare da Shabak, kasancewar lamarin babba ne, wanda ke nuna yadda abubuwa ke ƙara taɓarɓarewa. Za a gudanar da “dukkan bincin da ya kamata.”

A cewar Gidan Rediyon Sojan Isra’ila, tartsatsin wutar da ta tashi ba ta yi wata illa ba. Sai dai Gidan Rediyon Sojan da ‘yan sanda ba su yi wani ƙarin bayani kan daga inda aka jefa bama-baman ba.

Tun da farko, a ranar 19 ga watan Oktoba, ofishin Netanyahu ya ba da rahoton cewa an kai wani hari da jirigi mara matuƙi daga Lebanon zuwa gidan Netanyahu na Caesarea — harin da daga baya Hezbollah ta ɗauki alhakin kaiwa.

A lokacin ma, Netanyahu da iyalensa ba sa gidan, sannan ba a kunna jiniya ba a yankin kamar yadda kafofin watsa labaran Isara’ila suka rawaito.

Tun daga ƙarshen watan Satumba, Isra’i’a take kai manyan hare-hare Lebanon, tana nufar abin da ta yi iƙirari wuraren Hezbollah, abin da ke nuna yaƙin da ake yi tsakanin ɓangarorin biyu ya ƙara faɗaɗa.

Hukumomin lafiya na Lebanon sun ba da rahoton cewa tun daga watan Oktoban da ya gabata, hare-haren Isra’ila sun kashe fiye da mutum 3,400, sun jikkata kusan 14,7000, sannan sun raba fiye da mutum miliyan ɗaya da mahallansu.

Duk da gargaɗin da ƙasashen duniya suka riƙa yi cewa yakin zai iya rikiɗewa zuwa na yankin Gabas ta Tsakiya, Isra’ila ta ci gaba da faɗaɗa yakinta inda ta afka wa kudancin Lebanon a ranar 1 ga watan Oktoba.

TRT World