Wani mutum riƙe da wayar salula a Jami'ar Howard, inda 'yar takarar jam'iyyar Democrat Kamala Harris take gudanar da zaman jiran sakamakon zaɓe. / Hoto: Reuters

Dan takaran jam’iyyar Republican, Donald Trump da abokiyar fafatawarsa ta jam’iyyar Democrat, Kamala Harris, sun samu muhimman nasarori da yammacin Talata, inda Trump ya yi nasarar farko a daya daga cikin jihohin da ka iya fadawa a hannun kowa.

A halin yanzu dai Trump na gaba da Harris wurin samun kuri’un “wakilan masu zabe” 270 inda yake gaba da kuri’u 230 zuwa 210. Yayin da Harris ta kara jihohin California da Colorado da New Mexico da Oregon da kuma Washington cikin jihohin da ta yi nasara, Trump ya yi nasara a jihohin Idaho da Iowa da Kansas da kuma North Carolina, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Associated Press ya ruwaito.

Ana bukatar kuri’u 270 na wakilan masu zabe daga jihohi kafin mutum ya yi nasara a zaben shugaban kasan Amurka. Yawancin jihohi suna ba da dukkan kuri’unsu ne ga wanda ya yi nasara a fadin jiharsu, sai dai kuma jihohin Nebraska da Maine suna raba kuri’unsu ga ‘yan takara ne bisa sakamakon zabe a fadin jiha da kuma mazabun ‘yan majalisa.

Manazarta suna ganin fafatawa mai zafi a zaben shugaban kasa zai fi karkata ne a wasu jihohi kadan da ka iya fadawa a hannun ko wane dan takara— jihohin Arizona da Georgia da Michigan da Nevada da North Carolina da Pennsylvania da kuma Wisconsin— inda aka fin kankancin tazara a sakamakon zabukan jin ra’ayin jama’a.

An dai gama kada kuri’u a dukkanin jihohin bakwai din duk da cewa sakamakon jihar North Carolina ne kawai kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayyana a hukumance.

Yadda hankalin duniya ya koma kan zaɓen Amurka

Jirage marasa matuƙa na ta shawagi a sararin samaniya sannan gwanayen harbi daga ɓoye suna ta sa ido a yayin da miliyoyin Amurkawa suka kaɗa ƙuri'unsu a ranar Talata a zaɓen Amurka da ya fi kowanne jawo rarrabuwar kawuna a tarihi.

Mataimakiyar Shugaban Ƙasa Kamala Harris da ɗan takarar Jam'iyyar Republican Donald Trump suna fafatawa a zaɓen wanda ke matuƙar jan hankali.

Idan Trump ya yi nasara zai zamo shugaban ƙasa na farko da aka taɓa tuhuma da aikata manyan laifuka.

Trump zai kuma zamo shugaban ƙasa na biyu a tarihi da zai yi wa'adai biyu ba a jere ba a matsayin shugaban ƙasa, bayan Grover Cleveland a ƙarshen ƙarni na 19.

Ita kuwa Haris tana fatan zama mace ta farko, kuma mace baƙar fata ta farko, sannan 'yar asalin yankin Asiya ta farko da za ta shiga Fadar White House.

Jami'ai sun samar da matakan tsaro a rumfunan zabe a faɗin ƙasar a ƙoƙarinsu na tabbatar da cewa komai ya gudana cikin aminci.

Don ƙara ƙarfafa tsaro, an girke 'yan sanda da dama a kan tituna a faɗin ƙasar.

Trump yana kan gaba a zaɓen shugaban Amurka, Harris na biye da shi

'Yar takarar Democrat Kamala Harris da takwaranta na Republican Donald Trump suna fafatawa domin shiga Fadar White House, inda aka rufe rumfunan zaɓe ranar Talata sannan ake jiran tsammani na sakamakonsa.

Ƙwarya-ƙwaryar sakamakon zaɓen da kamfanin dillancin labaran The Associated Press ya tattara ya nuna cewa Trump yana kan gaba a jihohi 19, yayin da Harris ke kan gaba a jihohi goma.

Hakan na nufin Harris na da ƙuri'u 99 na wakilan da ke zaɓen shugaban ƙasa yayin da Trump ya samu ƙuri'u.

Ana buƙatar ƙuri'u 270 kafin mutum ya zama shugaban ƙasa.

Trump yana kan gaba a jihohi 9, Harris tana da jihohi 5 — ƙwarya-ƙwaryar sakamako

Ƙwarya-ƙwaryar sakamakon zaɓen da kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya tattara ya nuna cewa ɗan takarar shugaban Amurka na jam'iyyar Republican Donald J Trump yana kan gaba a jihohi tara, yayin da 'yar takara ta Democrat Kamala Harris take kan gaba a jihohi biyar.

Associated Press ya yi hasashen ne gabanin a kammala jefa ƙuri'a.

Miliyoyin Amurkawa ne suke kada ƙuri'a a fafatawar da ake yi tsakanin Trump da Harris.

Kazalika ana zaɓen 'yan majalisar dokokin tarayya.

2115 GMT — Ana ci gaba da zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa

Wakiliyar TRT World Zahra Yarali ta rawaito daga garin Fairview na jihar Virginia yadda masu fafutukar goyon bayan Falasdinawa suka fito a rumfunan zabe.

Sun isa rumfunan zabe biyar na yankin DMV (DC, Maryland, Virginia) inda suka rika kira ga masu kada kuri'a su tuna da kisan kare-dangin da Isra'ila take yi wa al'ummar Gaza kafin su jefa kuri'unsu.

Wata Ba'amurkiya 'yar asalin Falasdinu Hazami Barmada da sauran jama'a sun dauki kwalaye da ke alamta cewa ya kamata mutane su yi zabe na "dimokuradiyya.

Palestinian American activist Hazami Barmada.

1840 GMT An kama mutumin da ya yi barazana a rumfar zaɓe a New York

An kama wani mutum bayan ya yi mummunar barazana a wata rumfar zabe da ke garin Fowler a birnin New York.

“Bincike ya tabbatar da cewa wani namiji wanda aka taɓa tuhuma da babban laifi ya yi yunkurin kada kuri’a, kuma matsayinsa ya nuna cewa ba shi da rajista tun bayan da aka sako shi daga gidan yari,” in ji sanarwar da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar, inda ta kara da cewa mutumin ya fusata kuma ya fara yin "kalamai masu ban tsoro cewa zai ƙona wurin kuma zai dawo da bindiga."

‘’Yan sanda sun kaddamar da bincike don neman mutumin, wanda ya gudu daga wurin, amma jim kadan aka kama shi.” Sanarwar ta ce, ana ci gaba da gudanar da bincike.

1702 GMT — Donald Trump ya kada kuri'arsa a Florida

Donald Trump ya kada kuri'arsa a Palm Beach, Florida kuma ya ce yakin neman zabensa na baya-bayan nan shi ne mafi kyau.

Da yake magana da manema labarai, Trump ya ce yana da "kwarin gwiwa" zai " lashe zaben."

"Na gudanar da gagarumin yakin neman zabe, ina ganin watakila shi ne ya fi kyau a cikin ukun, mun yi aiki mai kyau a na farko, mun yi a na biyu amma wani abu ya faru, zan ce wannan shi ne mafi kyawun yakin neman zaben da muka gudanar," in ji shi, yana tsaye kusa da matarsa, Melania Trump.

Ya ce zai amince da shan kaye "idan zabe ne na gaskiya".

1329 GMT Ana ta ɗaukar matakai a Washington kan yiwuwar ɓarkewar rikici a zaɓen Amurka

Ana ta rufe harkokin kasuwanci a yankunan da ke kusa da Fadar White House stare da ɗaukar matakan tsaro yayin da ake taka tsantsan cikin fargabar ɓrkewar rikici a ranar zaben - da kuma kwanaki masu zuwa.

Magajin Garin DC Muriel Bowser ya ce hukumar 'yan sanda tana kuma ƙara ƙaimi a gundumomin kasuwanci da ke dukkan yankuna takwas na birnin.

Shugabar 'yan sandan birnin Pamela Smith a wani taron manema labarai ta kuma tabbatar wa mazauna birnin cewa sashenta ya shirya don tunkarar duk wani abu da ranar zabe za ta iya kawowa.

Ta ce, "Tawagarmu ta kasance da cikakkiyar himma da kuma taka tsantsan," in ji ta. "Mu ne mafi ƙwarewa a kasar nan kan abin da muke yi, kuma za mu ci gaba da aiki ba dare ba rana don kiyaye Washington DC, da kuma kiyaye mazaunanmu."

TRT World