Falasɗinawa ɗauke da kayansu suna kan hanyar yin gudun hijira bayan rundunar sojin Isra'ila ta umarce su su fita daga yankin da suke kira D5 a Gaza City / Photo: AA

Lahadi, 13 ga watan Oktoba, 2024

0959 GMT: Isra'ial ta kashe ƙarin Falasɗinawa 52 a Gaza, yayin da adadin mutuwa ya kai 42,200

Aƙalla ƙarin Falasɗinawa 52 ne suka halaka a wani hari ta sama da Isra'ila ta kai a Gaza, wanda hakan ya ƙara yawan mutanen da aka kashe tun bara zuwa mutum 42,227, cewar ma'aikatar lafiya ta yankin da ke ƙarƙashin mamaya.

Wata sanarwa daga ma'aikatar ta ce wasu ƙarin mutane 98,464 sun samu raunuka a hare-hare da ke cigaba da gudana.

“Sojojin Isra'ila sun kashe mutum 52 people kuma sun raunata mutum 128 a wani kisan kiyashi ya aka yi wa iyalai cikin awannin 24 da suka gabata,” in ji ma'aikatar.

Ta ƙara da cewa, “Mutane da dama suna maƙale ƙarƙashin baraguzan gine-gine, da kuma kan tituna yayin da masu ceto suka kasa cim musu.”

1040 GMT — Firaministan Isra'ila ya nemi MDD ta kwashe sojojin tabbatar da zaman lafiya daga Lebanon

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya nemi Majalisar Ɗinkin Duniya ta kwashe sojojin rundunar tabbatar da zaman lafiya daga wurare da ake artabu a Lebanon, wato rundunar UNIFIL.

Netanyahu ya ce sojojinsa sun nemi MDD ta kwashe sojojinta sau da dama, inda ya ƙara da cewa kasancewarsu a wajen tamkar suna ƙangin Hezbollah ne.

0845 GMT — Isra'ila na shirin kai wa Iran hari tare da haɗin-gwiwar Amurka wadda ta girke makaman tare makami mai linzami

Jaridun Isra'ila sun ruwaito cewa rundunar sojin Isra'ila suna shirya yiwuwar kai hari kan Iran, tare da haɗin gwiwar Amurka, bayan da Iran ta kai mata harin ramuwa na makamai masu linzami da Iran ta kai mata, a farkon watan nan.

A cewar tashar tashar Channel 12, Isra'ila "tuni ta yanke hukuncin nau'in matakin da za ta ɗauka kan Iran," duk da dai ba ta fayyace lokacin kai harin ba.

A yammacin Asabar, sojin Isra'ila sun sanar cewa an girke na'urar tare makami mai linzami da Amurka ta ƙera mai suna THAAD. A kawo na;urar cikin Isra'ila don magance barazanar harin makamai masu linzami masu dogon zango daga Iran.

0610 GMT — Isra'ila ta kai harin bam kan masallaci mai tarihi a kudancin Lebanon

A wasu jerin hare-hare da suka kai da duku-dukun yau, jiragen yaƙin Isra'ila sun kai farmaki kan wuarare da dama a kudancin Lebanon, inda suka yi ta'adi da rushe-rushe, a cewar Kamfanin dillancin labarai na ƙasar Lebanon.

Da kusan ƙarfe 3:45 na safiya wani harin jirgi ya ragargaza wani daɗaɗɗen masallaci a tsakiyar garin Kfar Tibnit, inda ya tarwatsa ginin, kamar yadda rahotannin suka nuna.

Tun da misalin ƙarfe 12:15 na safiyar, wani harin kan wani gini mai hawa uku kusa da tashar Ghabris, kan babban titin Zefta-Nabatieh, shi ma ya ruguza shi.

Harin ya tilasta rufe tituna sakamakon baraguzan gine-gine da suka tare hanya. Wani hari na uku kuma, da misalin ƙarfe 1:30 na safiya ya faɗa wa garin Aita al-Shaab.

Yaƙin da mahukuntan Tel Aviv suka kwashe shekara ɗaya suna yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,175. A gefe guda, hare-haren da isra'ila ta ƙadamar a Lebanon tun Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,255 da raba miliyan 1.2 da muhallansu.

2227 GMT — Hukumomin Gaza sun ce kisan kiyashin da Isra'ila take yi wani shiri ne na korar Falasɗinawa daga yankinsu

Ofishin Watsa Labarai na Gaza ya ce sojojin Isra'ila suna ƙara ƙaimi wajen kisan kiyashi a arewacin Gaza, ciki har da sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia, tare da "luguden wuta da gangan" tun da suka soma kai hare-hare ta ƙasa a ranar 6 ga watan Oktoba.

"Sojojin mamaya sun hana masu akin ceto da tawagar masu bayar da ɗaukin gaggawa kwashe gawawwaki fiye da 75 na shahidai daga cikin shahidai 285 da suka kashe a hare-hare ta ƙasa," in ji sanarwar da ofishin ya fitar.

Sojojin suna "aikata laifukan keta haƙƙin ɗan'adam da kuma yin kisa da gangan ta hanyar kai hare-hare da bama-bamai kan mutanen da suka raba da gidajensu da kuma cibiyoyin da suke samun mafaka, inda suke kashe fararen-hula da kuma kai hari kan taron mata da yara," a cewar sanarwar.

Ofishin ya ƙara da cewa a yunƙurinta na ci gaba da yin kisan kiyashi, rundunar sojojin Isra'ila ta yi yunƙurin rusa dukkan fannin kiwon lafiya a arewacin yankin ta hanyar hana asibitoci gudanar da ayyukansu tare da kai hare-hare a cikinsu.

Ya yi gargaɗi game da shirin Isra'ila na mayar da "arewacin Gaza zuwa wani yanki da za a ruguza tare da kashe ɗaukacin mazaunansa, a wani ɓangare na korar Falasɗinawa daga yankin."

0036 GMT — Amurka ta nuna damuwa dangane hare-haren Isra'ila kan ofisoshin MDD a Lebanon

Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin ya bayyana damuwa dangane da hare-haren Isra'ila a wajen da Ofisoshin Dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya na Wucin-gadi a Lebanon (UNIFIL) yake a kudancin Lebanon, yayin tattaunawar wayar tarho da suka yi da Minisatan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant.

Austin "ya bayyana babbar damuwarsa kan rahotannin da ke cewa dakarun Isra'ila sun yi harbi wajen da dakarun wanzar da zaman lafiya na MƊD suke a Lebanon tare da rahotannin da ke cewa sojojin Lebanon biyu sun mutu," a cewar kakakin Pentagon Pat Ryder a cikin wata sanarwa.

"Sakataren ya kuma jaddada muhimmancin tabbatar da tsaro da kare dakarun na UNIFIL da sojojin Lebanon, ya kuma jadda buƙatar dakatar da matakan soja a Lebanon zuwa matakan diflomasiyya a matsayin hanyar kawo karshen yakin cikin gaggawa," a cewar sanarwar.

TRT World