Wanda ake zargi da kai mummunan hari da mota cikin kasuwar sayayyar Kirsimeti yana da ra’ayin tsananin ƙyamar Musulunci, kuma yana jin haushin tsarin Jamus kan ‘yan ci-rani da masu neman mafaka, a cewar hukumomi, abin da ya sa masu tsattsauran ra’ayi suka ɓuge da borin kunya.
Ministar cikin gida Nancy Fraser ta faɗa a rana Asabar cewa yana da ra’ayin “ƙyamar Musulunci.”
Da farko har an fara kwatanta harin a kafafen sada zumunta da wani mummunan hari da wani dan ci rani ya kai a wata kasuwar kayan Kirsimeti a Berlin a 2016
Daga baya ta tabbata cewa maharin, ɗan Saudiyya, wani likitan ƙwaƙwalwa ne wanda ya zauna a Jamus tsawon shekara 18, yana sukar Musulunci kuma a baya ya nuna goyon baya ga masu tsattsauran ra’ayi a abubuwan da yake wallafawa a kafafen sada zumunta.
Hakan ya sa masu tsattsauran ra’ayin suka fara ɗaukar matakin borin kunya.
Martin Sellner, ɗan kasar Austria mai farin jini a Jamus, ya wallafa saƙo a shafukan sada zumunta inda ya ce dalilan da ake zargin su ne ssuka sa aka kai harin "da alama suna da sarƙaƙiya", ya ƙara da cewa wanda ake zargin "ya ƙyamaci addinin Musulunci, amma ya fi kyamar Jamusawa".
'Bakin ciki da kaduwa'
Shugabar jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayi ta Alternative for Germany (AfD), Alice Weidel, ta rubuta a kan X cewa: "Yaushe za a daina wannan hauka?"
"Abin da ya faru a yau ya shafi mutane da yawa. Ya shafe mu sosai," in ji Fael Kelion, dan Kamaru mai shekaru 27 da ke zaune a birnin, kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
"Ina ganin tun da (wanda ake zargin) baƙo ne, jama'a ba za su ji daɗi ba, ba za su sami karɓuwa ba."
Michael Raarig, mai shekaru 67 kuma injiniya, ya ce: "Na yi bakin ciki, na yi mamaki, da ban taba tunanin hakan na iya faruwa ba a nan garin na lardin Gabashin Jamus."
Ya ƙara da cewa ya yi imanin "jam'iyyar AfD za ta yi amfani da harin ", wadda ke da goyon bayanta mafi karfi a gabashin Jamus a da a baya 'yan gurguzu ne.
Harin da aka kai da mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar tare da jikkata sama da 200.
An tsaurara matakan tsaro a kasuwannin Kirsimeti a wasu wurare a Jamus a ranar Asabar, inda aka ga ƙarin ‘yan sanda a Hamburg da Leipzig da sauran garuruwa.