Sojojin Isra'ila 8 ne suka mutu a fadan da ake yi a kudancin Lebanon / Photo: AFP

Laraba, 2 ga Oktoban 2024

1436 GMT –– Sojojin Isra'ila takwas aka kashe a faɗan da aka gwabza a kudancin Lebanon, kamar yadda rundunar sojin Isra'ila ta fitar a cikin wata sanarwa.

0300 GMT — Iran da Isra'ila na yi wa juna barazana; Hezbollah ta daƙile harin ƙasa da Tel Aviv ta kai

Hezbollah ta ce ta yi arangama da sojojin Isra'ila da suka yi kokarin kutsawa cikin kasar Lebanon, tare da kai hari kan sojojin Isra'ila da ke kan iyakar kasar, a cewar sanarwar da kungiyar ta fitar.

Har ila yau, Hezbollah ta ce mayaƙanta sun kai hari kan "wani babban sansanin soji" a Misgav Am da ke kan iyaka da inda aka jibge "rokoki da manyan bindigogi", da kuma inda aka jibe sojoji a wasu wurare uku, inda rukuni daya ke da rokokin Burkan.

A Iran, babban hafsan hafsoshinta ya sha alwashin kai hare-hare kan ababen more rayuwa a fadin kasar Isra'ila idan har aka kai wa kasarsa hari, bayan da Tehran ta harba makami mai linzami kusan 200 kan abokan gabarta, wadda ke yakinta a Zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya tare da kai wa kasar Labanon hari ba ƙaƙƙautawa.

Manjo Janar Mohammad Bagheri ya fada a gidan talabijin na kasar cewa "za a maimaita kai karin da ƙarfi sosai kuma za a kai hari kan dukkanin kayayyakin aikin gwamnati."

Bagheri ya ce Tehran ta kai zuciya nesa bayan da Amurka da EU suka yi alkawarin tsagaita wuta a Gaza biyo bayan kisan da aka yi wa shugaban siyasar Hamas Ismail Haniyeh, ya kara da cewa "a yanzu ba za ta zura ido ba" bayan da Isra'ila ta kashe shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah da Birgediya Janar Abbas Nilforoushan na Iran.

TRT World