Makamai masu linzami da aka harba daga Iran zuwa Isra'ila sun yi ta gilmawa a sararin samaniya kamar yadda aka gani daga Deir al-Balah na Gaza. / Hoto: AP

Iran ta harba ɗarutuwan makamai masu linzami cikin Isra'ila yayin da Tel Aviv ke ci gaba da yaƙi a Gaza da Lebanon.

An fara kai harin ne da misalin karfe 4:45 na yamma agogon GMT a ranar Talata, inda kafafen yada labaran Iran sun ce kawo yanzu an harba makamai masu linzami akalla 400.

A cikin wata sanarwa ta farko da ta fitar, Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ce harin na martani ne ga kashe shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniyeh da shugaban kungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah, da kwamandan IRGC Abbas Nilforoshan.

An kashe Haniyeh a Tehran a watan da ya gabata. An kashe Nasrallah ne a Beirut ranar Juma'a tare da Nilforoshan.

Dakarun na IRGC sun yi gargadin cewa idan Isra'ila ta mayar da martani kan harba makamai masu linzamin, to za ta fuskanci karin "munanan hare-hare."

Sannan ta ce ana kai harin ne tare da goyon bayan sojoji da Ma'aikatar Tsaro.

'Ba a jikkata sosai ba'

Kakakin sojin Isra'ila ya ce mutane ƙalilan ne suka ji raunuka bayan harin makamai masu linzami da Iran ta kai, kuma jama'a na iya ficewa daga wuraren da aka jefa bama-bamai.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta daƙile wani adadi mai yawa na makamai masu linzamin da Iran ta harba a kasar, kakakin rundunar ya ce wurare kaɗan hare-haren suka samu.

Kakakin rundunar sojin Isra'ila Rear Admiral Daniel Hagari ya ce "Mun daƙile makaman da dama. Wasu hare-hare sun shafi tsakiyar yankin da wasu yankuna a kudancin kasar."

Ta hanyar harba makami masu linzami kan Isra'ila, Iran ta dauki mataki "bisa doka da dacewa, kuma na halal" kan Isra'ila, in ji tawagar Tehran ta Majalisar Dinkin Duniya a ranar Talata.

Sanarwar tawagar a shafin X ta ƙara da cewa: "Iran ta aiwatar da martani bisa doron shari'a, da dacewa da kuma halastaccen martani ga ayyukan ta'addanci na gwamnatin masu tsaurin aƙidar kafa ƙasar Isra'ila da ta haɗa da kai wa al'ummar Iran da muradunsu hari da kuma keta hurumin kasar Iran."

Sanarwar ta kara da cewa, "Idan har gwamnatin masu tsaurin aƙidar kafa ƙasar Isra'ila ta kuskura ta mayar da martani ko kuma ta ci gaba da aikata munanan laifuka, to za a samu martani mai muni. Ana shawartar ƙasashen yankin da magoya bayan masu tsaurin aƙidar kafa ƙasar Isra'ila da su raba hanya da gwamnatin."

TRT World