Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta soma kai "taƙaitattun" hare-hare ta ƙasa a Lebanon, tana mai cewa za ta ci gaba da kai su daidai gwargwado amma ba kamar yadda take yi a yaƙin Gaza ba.
Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ranar Talata da sanyin safiya ta ce "kamar yadda shugabannin siyasa suka amince, a 'yan awannin da suka gabata, IDF (rundunar soji) ta soma kai taƙaitattun hare-hare ta ƙasa kan wasu keɓaɓɓun wurare na Hezbollah da ke kudancin Lebanon bayan samun bayanan sirri."
"Waɗannan wurare suna cikin ƙauyukan da ke kusa da kan iyaka kuma suna barazana ga al'ummomin Isra'la da ke yankin arewacin Isra'ila," in ji sanarwar.
Rundunar sojin ta ce tana kai hare-haren ne "bisa tsari da Babban Jami'in Tsaro da Kwamandan yankin Arewa suka gindaya, wanda aka bai wa sojojin IDF horo a kansa a watannin baya bayan nan."
Sanarwar ta ce, "Rundunar Sojin Sama ta Isra'ila da makaman atilari na IDF suna taimaka wa dakarun ƙasa domin kai hare-hare a inda aka nufa ba tare da akucewa ba."
Da take magana a game da hare-haren, sanarwar ta ƙara da cewa "hare-haren da aka yi wa laƙabi da operation 'Northern Arrows' zai ci gaba kamar yadda aka tsara amma ba zai kasance irin yaƙin Gaza ba."