Cikin fargabar ɓarkewar yaƙi da wani jami'in Fadar White House ya yi hasashen Iran za ta kai harin makami mai linzami kan Isra'ila, ga wani nazari na gaggawa kan irin karfin makami mai linzamin da Tehran ke da shi a cikin tarin makamanta na soja.
A cewar wani rahoto na shekarar 2022 da rundunar sojin Amurka ta bayar, Iran na da makamai masu linzami sama da 3,000, wadanda ke da nau'uka daban-daban - daga masu cin gajeren zango da matsakaita, zuwa makamai masu linzami masu amfani da man fetur da farko da suka dogara da waɗanda aka kwaikwaya daga fasahar Koriya ta Arewa da Rasha.
Makamai masu linzami na Sajjil, wadanda ke amfani da fasahar sarrafa mai, za su iya daukar nauyin kilogiram 700 kuma su yi tafiyar nisan kilomita 2,500 daga yankin Iran. Tel Aviv kuwa na da tazarar kilomita 2,000 ne kawai daga Tehran.
Wani makami mai linzamin da shi kuma ake kira Khaibar, shi ma zai iya tafiyar mil 1,240 tare da ɗaukar abin da ya kai nauyin kilo 2,000.
Iran na yawan amfani da jerin makamai nau'in Shahab don gigita maƙiyanta. Makami mai linzami na Shahab-3 na iya tafiyar kusan kilomita 900. Duk da yake yawanci ana amfani da su don sanya tsoro a cikin birane da kuma firgita abokan gaba, asarar da waɗannan nau'in makaman za su iya haifar ba ta kai ra Sajjil ba.
Za a iya harba makami mai linzamin na Sajjil da ire-irensa na Qiam cikin kankanin lokaci da kuma motsa shi daga wannan wuri zuwa wani da taimakon ƙananan motoci.
A cikin shekaru 20 da suka gabata, Iran ta inganta fasaharta wajen ƙera makamai masu linzami. Misali, an bai wa nau'in makamai na Fateh-110 cikakken daidaito wajen kai hari kan cibiyoyin soji, kamar yadda aka tabbatar da harin da Iran ta kai kan sojojin Amurka a Iraƙi a watan Janairun 2020.
A cikin watan Janairun 2024, Iran ta kuma kai hari da makami mai linzami kan abin da ta bayyana a matsayin "sassan leken asiri" na Isra'ila a yankin Erbil na arewacin Iraki. Sai dai wani jami'in Amurka daga baya ya ce harin bai yi nasara ba kamar yadda gwamnatin Iran ta yi iƙirari, yana mai cewa makami mai linzamin "bai saita daidai ba".
A ci gaba da harin makami mai linzami da Iran ta kai, Tel Aviv ta kasance cikin shirin ko ta kwana. Amurka, kamar yadda ta saba, ta zo taimakon Isra’ila, tana taimaka wa sojojin Isra’ila wajen daƙile duk wani makami da Iran ta harba.
A wani hari makamancin wannan da Iran ta kai a watan Afrilu, Amurka ta ce an yi nasarar kawar da mafi yawan wadannan makamai masu linzami.