Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a kullum a Gaza waɗanda akasarinsu mata ne da yara. / Hoto: AA

0837 GMT — Kimanin Falasdinawa 20 da suka hada da yara da dama ne aka kashe a hare-haren da Isra'ila ta kai cikin dare a Gaza, in ji likitoci.

Kakakin hukumar kiyaye farar hula Mahmoud Basal ya ce an tsamo gawawwakin mutum 18 daga karkashin baraguzan gidaje uku bayan harin da Isra'ila ta kai a birnin Gaza da kuma arewacin yankin.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce akwai yara bakwai daga cikin wadanda lamarin ya shafa.

A gefe guda kuma, an kashe miji da matarsa ​​a wani harin da Isra'ila ta kai gidansu da ke sansanin 'yan gudun hijira na Maghazi da ke tsakiyar Gaza, kamar yadda wata majiyar lafiya ta bayyana.

0816 GMT — Dakarun Isra'ila sun tsare aƙalla Falasdinawa 14 daga yankuna daban-daban na Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.

Daga cikin wadanda ake tsare da su har da wata mata 'yar Gaza da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan wadda ta je can domin neman magani, baya ga yara da wadanda ake tsare da su.

Baya ga haka Isra’ila ta sake kai hari kan wani gida da ke Jabalia a arewacin Gaza da aka yi wa ƙawanya, inda sojojin na Isra’ila suka kashe aƙalla Falasɗinawa 10, kamar yadda majiyoyin kiwon lafiya suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters

TRT Afrika da abokan hulda