Wani bam da aka ɓoye a jikin babur mai amfani da lantarki ya kashe wani babban janar na ƙasar Rasha wanda ke kula da jami'an tsaron nukiliya a birnin Moscow a ranar Talata, kamar yadda kwamitin bincike na Rasha ya bayyana.
Fashewar bam ɗin ta kashe Laftanar Janar Igor Kirillov, wanda shi ne babban hafsan sojin Rasha kan Nukiliya da rundunar da ke sa ido kan sinadarai da makamai masu guba, a wajen wani gini da ke Ryazansky Prospekt, wanda ke kan hanyar da ta kai kusan kilomita 7zuwa kudu maso gabashin Kremlin.
"An kashe Igor Kirillov, shugaban jami'an rundunar sinadarai makamai masu haɗari na sojojin Rasha da mataimakinsa." a cewar binciken Kwamitin.
Hotunan da aka yaɗa a shafukan Telegram na Rasha sun nuna yadda wata kofar shiga ginin ta ruguje da kuma gawarwaki biyu da ke kwance cikin jini a kan dusar kankara.
Tuni dai aka soma binciken laifin.
Dakarun sojin Rasha a fannin sa ido kan makamai da sanadarai masu guba, da aka sani da RKhBZ, runduna ce ta musamman da ke da alhakin sa ido kan yanayin haɗarin makamai da sinadarai masu guba.