Hamas / Photo: AA

Talata, 17 ga watan Disamba, 2024

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce tattaunawar da aka yi a Doha babban birnin Qatar, don cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni da Isra'ila, akwai alamun ta yi nasara kuma da gaske ake yi.

Sanarwar ta kara da cewa, "Samun yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni mai yiyuwa ne idan Isra'ila ta daina sanya sabbin sharudda."

A cikin 'yan kwanakin nan, kafofin watsa labarai na Isra'ila sun ba da rahoton "ci gaba" a tattaunawar kai tsaye da Hamas da nufin cim ma yarjejeniya.

Jami'an Amurka da na Isra'ila su ma suna nuna kyakkyawan fatan cewa tattaunawar da kasashen Masar da Qatar suka kulla na iya cim ma matsaya a karshen wannan wata amma kuma sun yi gargadin cewa tattaunawar na iya rugujewa.

A ranar Litinin Ministan Tsaron Isra'ila Isra'ila Katz ya ce an kusa cim ma yarjejeniyar tsagaita da musayar fursunoni da Hamas.

0720 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 14 a sabbin hare-hare da ta kai a Gaza

Isra'ila ta kai ƙarin hare-hare a faɗin yankin Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 14, 10 daga cikinsu a gida ɗaya a Birnin Gaza, kamar yadda ma'aikatan kiwon lafiya suka bayyana. Hakan na faruwa ne a yayin da dakarun Isra'ila suke ci gaba da kutsawa kudancin Rafah.

Ma'aikatan kiwon lafiya sun ce dakarun Isra'ila sun kai hari a wani gida a unguwar Daraj da ke wajen Birnin Gaza inda suka lalata shi tare da gidajen da ke kusa da shi.

Kazalika dakarun na Isra'ila sun kashe mutum huɗu a hare-hare biyu da suka kai ta sama a birnin da kuma garin Beit Lahia da ke arewacin yankin, in ji ma'aikatan kiwon lafiya.

Kawo yanzu rundunar sojojin Isra'ila ba ta ce uffan ba game da waɗannan hare-hare.

A yankin Rafah, kusa da kan iyaka da Masa, tankokin yaƙin Isra'ila sun ci gaba da kutsawa inda suka nufi yankin Mawasi da ke yammaci, wanda ana ayyana a matsayin tudun-mun-tsira.

Sun riƙa buɗe wuta a yayin da suke tilasta wa mazauna yankin tserewa zuwa arewaci inda Khan Younis yake.

Ƙarin labarai👇

2116 GMT — Isra'ila ta kashe wani Bafalasɗine, ta jikkata gommai a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan

Isra'ila ta kashe wani Bafalasɗine tare da jikkata gommai a samane da ta kai Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.

Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Falasɗinu ta ce "mutum da ya yi shahada yana ƙoƙarin isa Asibitin Gwamnati na Rafidia daga Nablus bayan ya bar sansanin 'yan gudun hijira na Askar."

Ƙungiyar Bayar da Agaji ta Palestinian Red Crescent Society, wadda tun da farko ta fitar da sanarwar jikkata wani matashi a wani tsauni da ke kusa da sansanin Askar, ta tabbatar da cewa dakarun Isra'ila sun hana ma'aikatan kiwon lafiya isa wurin.

TRT World