Juma'a, 11 ga Oktoban 2024
1614 GMT — Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, sama da mutum 420,000 galibi ‘yan kasar Syria ne suka tsallaka zuwa Syria daga Lebanon tun farkon hare-haren Isra’ila.
Sama da ‘yan kasar Syria 310,000 da ‘yan kasar Lebanon 110,000 ne suka tsallaka zuwa Syria a ranar 23 ga watan Satumba zuwa 9 ga watan Oktoba, in ji Ravina Shamdasani, mai magana da yawun ofishin kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya, a wani taron manema labarai a Geneva.
Da yake cewa Isra'ila ta kai harin bam mafi girma a yau a tsakiyar birnin Beirut a daren jiya, Shamdasani, ya nakalto Ma'aikatar Lafiya ta Lebanon, ya ce akalla mutum 22 ne suka mutu, wasu fiye da 100 kuma suka jikkata.
1250 GMT — Hare-haren sama na Isra'ila sun sake kashe mutum 11 a kudanci da gabashin Lebanon
Aƙalla mutum 11 ne suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai kan garuruwan kudanci da gabashin Lebanon.
Kamfanin dillancin labaran Lebanon ya rawaito cewa an kashe wasu ‘yan kasar huɗu a wani harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan wani ginin mazauna garin Jebchit da ke kudancin yankin Nabatieh.
Kafar ta kara da cewa akalla mutane biyar ne suka mutu sannan wasu biyu suka jikkata a wani harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan wani gida a yankin Baalbek-Hermel da ke gabashin kasar.
A birnin Tyre, wata mata ta mutu sakamakon raunukan da ta samu kwanaki da suka gabata a wani harin da jiragen Isra'ila suka kai a gidanta, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar ya ruwaito.
0546 GMT — Indonesia ta ce harin da Isra'ila ta kai ya jikkata ma'aikatanta 2
Indonesia ta tabbatar cewa biyu daga cikin sojojinta masu aikin wanzar da zaman lafiya a ƙarƙashin shirin Majalisar Ɗinkin Duniya sun jikkata a wani hari da Isra'ila ta kai Lebanon, sannan ta ce harin ya keta dokokin ƙasashen duniya.
"A harin da aka kai a wani dogon gini a Nakura, an jikkata jikkata ma'aikatan wanzar da zaman lafiya biyu, kuma 'yan ƙasar Indonesia ne," in ji wata sanarwa da Ministar Harkokin Waje Retno Marsudi ta fitar.
Ta ƙara da cewa an garzaya da mutanen da suka jikkata zuwa wani asibiti.
"Indonesia ta yi Allah wadarai da wannan hari da babbar murya," in ji ta. "Kai hari kan ma'aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya da gininta babban keta dokokin Ƙasashen Duniya ne."
0130 GMT — Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai munanan hare-hare a Yammacin Gaɓar Kogin Jordan da ta mamaye
Jiragen yakin Isra'ila sun harba makamai masu linzami da suka kashe Falasdinawa biyu a yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.
Kamfanin dillancin labaran Falasdinu na WAFA ya rawaito cewa, an kashe 'yan kasar biyu a wani harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai kan wata mota a yankin Jabal al Salihin da ke tsakanin yankin Dhannabah da kuma sansanin 'yan gudun hijira na Nur Shams da ke gabashin Tulkarem.
Majiyoyin sun kara da cewa nan take sojojin Isra'ila suka kai farmaki a yankin bayan sun kai farmakin, inda suka kwashe gawarwakin mutanen, sannan suka janye daga wurin.
Tun da fari da yammacin wannan rana ne sojojin Isra'ila suka kai farmaki kan sansanin 'yan gudun hijira na Nur Shams tare da ƙaƙaba wa sansanin ƙawanya kafin su kai hare-hare.
Karin bayani 👇
0100 GMT — Manyan jami'an tsaron Isra'ila sun gana a cikin Lebanon
Rundunar sojin Isra'ila ta bayyana cewa, babban hafsan hafsoshin sojin kasar Herzi Halevi da daraktan Shin Bet Ronen Bar sun gudanar da wani bincike na hadin gwiwa a kudancin kasar Lebanon a karon farko.
Sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta ce Halevi da Bar "sun gudanar da wani bincike na hadin gwiwa tare da dakarun da ke yaki a kudancin Lebanon, tare da kwamandan rundunar sojojin arewa da kuma kwamandan runduna ta 91."
A cewar jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra'ila, wannan shi ne karo na farko da manyan jami'an tsaro ke gudanar da taro a cikin Lebanon.