Isra'ila ta kashe dubban Falasɗinawa a hare-haren da ta kwashe fiye da watanni goma sha biyar tana kai a a yankinsu. / Hoto: AA

Laraba, 5 ga Fabrairu, 2025

0530 GMT –– Wani jami'in Hamas Sami Abu Zuhri ya ce kalaman da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na neman ƙwace ikon tafiyar da harkokin yankin Gaza 'zancen banza' ne kuma 'abubuwan ƙyama'.

"Kalaman Trump game da buƙatarsa ta karɓe ikon Gaza zancen banza ne kuma abin ƙyama, sannan duk wani tunani irin wannan yana iya haddasa rikici a yankin," in ji Abu Zuhri a hira da kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Ƙarin labarai👇

0749 GMT — Hamas ta ce kalaman Trump na 'wariyar launin fata' game da Gaza shiri ne na 'kawar da fafutukar Falasɗinawa'

Ƙungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta yi fatali da buƙatar shugaban Amurka Donald Trump ta neman "ƙwace ikon tafiyar da" yankin Gaza waɗanda ta yi mamakin yinsu, sannan ta ce hakan "wariyar launin fata ce" da ke da nufin kawar da fafutukar Falasɗinawa.

"Matsayar mai nuna wariyar launin fata na Amurka ta yi daidai da ta masu tsaurin ra'ayi na Isra'ila da ke son kawar da mutanenmu tare da shafe gwagwarmayarmu," a cewar wata sanarwa da kakakin Hamas Abdel Latif al-Qanou ya fitar.

0219 GMT — Saudiyya ta jaddada goyon bayanta ga Falasɗinawa, ta yi watsi da buƙatar Trump

Saudiyya ta jaddada cewa ba za ta ƙulla wata alaƙa da Isra'ila ba muddin ba a kafa ƙasar Falasɗinu ba mai cin gashin kanta ba, sannan ta yi watsi da iƙirarin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa mahukunta a Riyadh sun sassauta matsayarsu.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta fitar da wata sanarwa da ke jaddada masayar masarautar ta "yin tsayin-daka ba tare da shayin kowa ba" bayan iƙirarin da Trump yayin ganawarsa a Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a Fadar White House.

A lokacin da aka tambaye shi kan ko Saudiyya ta buƙaci kafa ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta, Trump, wanda ke aune tare da Netanyahu a Fadar shugaban ƙasa ya ce: "A'a, ba su yi hakan ba."

"Ma'aikatar Harkokin Waje tana jaddada matsayar Masarautar Saudiyya ta kafa ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta ba tare da shayin kowa ba", in ji sanarwar da ma'aikatar ta fitar.

"Mai Girma Yarima Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud, Yarima Mai Jiran Gadon Sarauta kuma Firaminista, ya bayyana matsayarmu ƙarara kuma ba tare da tsoro ba a jawabin da ya gabatar na buɗe taron Majalaisar Shura karo na tara ranar 18 ga watan Satumba, 2024."

Sanarwar ta ƙara da cewa yarima ya sake jaddada matsayar masarauta a lokacin taron Ƙasashen Larabawa da Musulmai a Riyadh ranar 11 ga watan Nuwamban 2024, inda ya nanata buƙatar samar da ƙasar Falasɗinu mai iyaka kamar yadda take a 1967 da kuma kawo ƙarshen mamayar da Isra'ila take yi wa yankin Falasɗinu.

"Masarautar Saudiyya tana sake jaddada goyon bayanta kuma ba za ta sauya matsayarta ba komai zai faru kuwa.

"Masarautar Saudiyya tana sake jaddada goyon bayanta kuma ba za ta sauya matsayarta ba komai zai faru kuwa," in ji mahukuntan Riyadh.
TRT World