Abu Rudeineh ya yi kira ga Amurka ta sa baki cikin gaggawa domin "tsayar da hare-haren da Isra'ila take kai wa al'ummar Falasdinu, waɗannan za su ta'azzara yanayin da ake ciki." ./ Photo: AP

Litinin, 3 ga watan Fabrairu, 2025

1028 GMT — Fadar shugaban ƙasar Falasdinu ta zargi Isra'ila da "kawar da mutanen" Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.

"Hare-haren da Isra'ila take kai wa a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan sun kashe mutane 29, tare da jikata ɗaruruwan mutane da kama wasu, baya ga ruguza ɗaukacin rukunin gidaje a sansanin Jenin da na Tulkarem, da kuma raba dubban mutane da gidajensu," in ji Nabil Abu Rudeineh, kakakin Fadar shugaban ƙasar Falasdinu, a wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na WAFA ya wallafa.

Abu Rudeineh ya yi kira ga Amurka ta sa baki cikin gaggawa domin "tsayar da hare-haren da Isra'ila take kai wa al'ummar Falasdinu, waɗannan za su ta'azzara yanayin da ake ciki."

2133 GMT — Isra'ila tana yin luguden wuta a sansanin Jenin kamar yadda ta yi a Gaza — Falasɗinu

Isra'ila tana yin luguden wuta a gidajen jama'a da ke sansanin 'yan gudun hijira na Jenin kamar yadda ta yi a yankin Gaza da ta mamaye, in ji wani jami'in Falasɗinu a hira da kamfanin labarai na Anadolu Agency.

Kamal Abu al Rub, gwamnan Jenin da ke Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, ya ce hukumomin Isra'ila suna aiki tuƙuru domin ruguza sansanin ta yadda ba za a iya zama a gidaje da sauran matsugunan da ke cikinsa ba.

"Sojojin Isra'ila sun karkata zuwa Gaɓar Yammacin Kogin Jordan daga Zirin Gaza a yaƙin da suke yi, kuma abin da ke faruwa a sansanin Jenin ya yi kama da kisan ƙare-dangin da Isra'ila ta yi a Gaza," in ji shi.

Abu al Rub ya ƙara da cewa hare-haren bama-baman da Isra'ila take yi a sansanin si ne irinsa "na farko tun shekarar 2002, bayan yaƙin da ya lalata sansanin a wancan lokacin."

Hayaƙi ya turnuƙe a sansanin Jenin a yayin da Isra'ila take ci gaba da luguden wuta a yankin na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan. / Hoto: AA

0110 GMT — Trump ya ce tattaunawar da ake yi da Isra'ila da sauran ɓangarori kan Gabas ta Tsakiya tana samun 'ci gaba'

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce tattaunawar da ake yi tsakanin Isra'ila da sauran ƙasashe kan Gabas ta Tsakiya samun "ci gaba," gabanin tattaunawa Washington game da zagaye na gaba na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

"Tattaunawar da ake yi a kan Gabas ta Tsakiya tsakanin Isra'ila da sauran ƙasashe tana samun ci gaba. Bibi (Benjamin) Netanyahu' zai zo ranar Talata, kuma ina gani muna da manyan taruka da za mu yi," in ji Trump a hira da manema labarai, game da ziyarar firaiministan Isra'ila.

TRT World