Trump da Netanyahu  sun gudanar da taron haɗin-gwwiwa na manema labara a Fadar White House a Washington ranar 4 ga watan Fabrairun 2025. / Hoto: Reuters

Shugaba Donald Trump ya ce Amurka za ta karɓe ikon gudanar da harkokin yankin Gaza wanda yaƙi ya ɗaiɗaita, a yayin da ya gudanar da taron manema labarai a Fadar White House bayan ya tattauna da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu game da yaƙin da yake yi na kisan ƙare-dangi a Gaza.

"Amurka za ta karɓe ikon tafiyar da harkokin Zirin Gaza kuma za ta yi aiki mai kyawu a yankin. Za mu mallake shi. Kuma za mu ɗauki alhakin lalata dukkan bama-bama masu hatsari da ba su fashe ba da kuma sauran wuraren ajiye makamai," in ji Trump a kalaman da ya yi ranar Talata waɗanda suka jawo ce-ce-ku-ce.

Ya yi iƙirarin cewa "duk wadanda na yi magana da su sun yarda da batun Amurka na son mallakar wancan ƙasar."

Ya ce bai kamata "waɗancan mutane", wato ƙungiyar gwagwarmaya ta Hamas, su kasance waɗanda za su sake ginawa da kuma komawa yankin ba.

"Za mu yi abin da ya kamata," in ji Trump da yake magana game da tura dakarun ƙasarsa zuwa Gaza. "Idan akwai buƙatar hakan, za mu ɗauki mataki." Ya ce mutane daga sassan duniya za su zauna a yankin Gaza idan aka kammala sake gina shi.

Trump ya ƙara da cewa Amurka za ta rushe gine-ginen da ke yankin sannan ta "ƙirƙiro da sabon tsarin tattalin arziki da zai samar da ayyuka marasa iyaka da gidaje da ke yankin."

"Ina ƙaunar Isra'ila. Zan kai ziyara can kuma zan ziyarci Gaza da Saudiyya da sauran wurare da ke yankin Gabas ta Tsakiya," kamar yadda Trump ya shaida wa manema labarai, ba tare da bayyana lokacin da zai yi hakan ba.

Trump ya jaddawa waɗannan kalamai ne bayan ya yi irinsu kwanakin baya inda ya bayar da shawarar kwashe Falasɗinawa daga yankin Gaza "dindindin" tare da tsununar da su a ƙasashen Masar da Jordan.

TRT World