An kama mutumin da ya yi barazana a rumfar zaɓe a New York: AP / Hoto: Reuters / Photo: AFP

Yadda hankalin duniya ya koma kan zaɓen Amurka

Jirage marasa matuƙa na ta shawagi a sararin samaniya sannan gwanayen harbi daga ɓoye suna ta sa ido a yayin da miliyoyin Amurkawa suka kaɗa ƙuri'unsu a ranar Talata a zaɓen Amurka da ya fi kowanne jawo arrabuwar kawuna a tarihi.

Mataimakiyra Shugaban Ƙasa Kamala Harris da ɗan takarar Jam'iyyar Republican Donald Trump suna fafatawa a zaɓen wanda ke matuƙar jan hankali.

Idan Trump ya yi nasara zai zamo shugaban ƙasa na farko da aka taɓa tuhuma da aikata manyan laifuka.

Trump zai kuma zamo shugaban ƙasa na biyu a tarihi da zai yi wa'adai biyu ba a jere ba a matsayin shugaban ƙasa, bayan Grover Cleveland a ƙarshen ƙrni na 19.

Ita kuwa Haris tana fatan zama mace ta farko, kuma mace baƙar fata ta farko, sannan 'yar asalin yankin Asiya ta farko da za ta shiga Fadar White House.

Jami'ai sun samar da matakan tsaro a rumfunan zabe a fadin ƙasar a ƙoƙarinsu na tabbatar da cewa komai ya gudana cikin aminci.

Don ƙara ƙarfafa tsaro, an girke 'yan sanda da dama a kan tituna a faɗin ƙasar.

1840 GMT An kama mutumin da ya yi barazana a rumfar zaɓe a New York

An kama wani mutum bayan ya yi mummunar barazana a wata rumfar zabe da ke garin Fowler a birnin New York.

“Bincike ya tabbatar da cewa wani namiji wanda aka taɓa tuhuma da babban laifi ya yi yunkurin kada kuri’a, kuma matsayinsa ya nuna cewa ba shi da rajista tun bayan da aka sako shi daga gidan yari,” in ji sanarwar da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar, inda ta kara da cewa mutumin ya fusata kuma ya fara yin "kalamai masu ban tsoro cewa zai ƙona wurin kuma zai dawo da bindiga."

‘’Yan sanda sun kaddamar da bincike don neman mutumin, wanda ya gudu daga wurin, amma jim kadan aka kama shi.” Sanarwar ta ce, ana ci gaba da gudanar da bincike.

1702 GMT — Donald Trump ya kada kuri'arsa a Florida

Donald Trump ya kada kuri'arsa a Palm Beach, Florida kuma ya ce yakin neman zabensa na baya-bayan nan shi ne mafi kyau.

Da yake magana da manema labarai, Trump ya ce yana da "kwarin gwiwa" zai " lashe zaben."

"Na gudanar da gagarumin yakin neman zabe, ina ganin watakila shi ne ya fi kyau a cikin ukun, mun yi aiki mai kyau a na farko, mun yi a na biyu amma wani abu ya faru, zan ce wannan shi ne mafi kyawun yakin neman zaben da muka gudanar," in ji shi, yana tsaye kusa da matarsa, Melania Trump.

Ya ce zai amince da shan kaye "idan zabe ne na gaskiya".

1329 GMT Ana ta ɗaukar matakai a Washington kan yiwuwar ɓarkewar rikici a zaɓen Amurka

Ana ta rufe harkokin kasuwanci a yankunan da ke kusa da Fadar White House stare da ɗaukar matakan tsaro yayin da ake taka tsantsan cikin fargabar ɓrkewar rikici a ranar zaben - da kuma kwanaki masu zuwa.

Magajin Garin DC Muriel Bowser ya ce hukumar 'yan sanda tana kuma ƙara ƙaimi a gundumomin kasuwanci da ke dukkan yankuna takwas na birnin.

Shugabar 'yan sandan birnin Pamela Smith a wani taron manema labarai ta kuma tabbatar wa mazauna birnin cewa sashenta ya shirya don tunkarar duk wani abu da ranar zabe za ta iya kawowa.

Ta ce, "Tawagarmu ta kasance da cikakkiyar himma da kuma taka tsantsan," in ji ta. "Mu ne mafi ƙwarewa a kasar nan kan abin da muke yi, kuma za mu ci gaba da aiki ba dare ba rana don kiyaye Washington DC, da kuma kiyaye mazaunanmu."

TRT World