"Wannan hari ne na Isra'ila. Sojojin Amurka ba su da hannu kai tsaye," in ji Sakataren Yada Labarai na Rundunar Sojojin Sama Manjo Janar Pat Ryder ga manema labarai. / Hoto: Reuters

Juma'a, 18 ga Oktoban 2024

2210 GMT — Sojojin Amurka “ba su da hannu kai-tsaye” a kisan da Isra’ila ta yi wa Shugaban Hamas Yahya Sinwar, in ji Ma’aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon.

"Wannan hari ne na Isra'ila. Sojojin Amurka ba su da hannu kai-tsaye," in ji Sakataren Yada Labarai na Rundunar Sojojin Sama Manjo Janar Pat Ryder ga manema labarai.

Karin labarai 👇

0258 GMT — Amurka ta sake yin kira ga Isra'ila ta janye gaba daya daga Gaza bayan kawo karshen yaki

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta nanata cewa "A karshe" tana son ganin Isra'ila ta janye gaba daya daga yankin Gaza da ta yi wa ƙawanya.

Hakan ya biyo bayan kalaman da ɗan adawar Isra'ila Benny Gantz ya yi, wanda ya ba da shawarar cewa sojojin Isra'ila su ci gaba da kai farmaki a Gaza tsawon shekaru.

"A karshe muna son ganin Isra'ila ta janye gaba daya daga Gaza," in ji kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Matthew Miller, a lokacin da kamfanin dillancin labaran Turkiyya na Anadolu ya tambaye shi game da kalaman Gantz.

2127 GMT — Hezbollah ta sanar da wani sabon yanayi, ''na ta'azzara'' a yaƙi da Isra'ila

Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta sanar da "sauya wani sabon mataki a cikin arangamarta da Isra'ila".

A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta ce asarar da sojojin Isra'ila ta yi ta kai adadin mutuwar mutume 55 tare da jikkata sojoji da jami'ai sama da 500 tun daga ranar 1 ga watan Oktoba.

2130 GMT - Biden da Harris sun yi martani kan kisan Sinwar

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana kisan da Isra'ila ta yi wa shugaban Hamas Yahya Sinwar a matsayin wani muhimmin mataki, yana mai cewa hakan ya kawar da wani muhimmin cikas ga yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma yarjejeniyar sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

Mataimakiyar Shugaban Ƙasa Kamala Harris, 'yar takarar Jam'iyyar Democrat a zaben Amurka na watan Nuwamba, ta ƙara da cewa hakan wata dama ce ta "karshe ta kawo karshen yakin Gaza."

2100 GMT - Netanyahu na Isra'ila ya ce kisan Sinwar 'matakin farko ne na kawo ƙarshen' yakin Gaza

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fada a yammacin jiya Alhamis cewa kisan shugaban Hamas Yahya Sinwar shi ne "mafarin kawo karshen" yakin Gaza.

A cikin wata sanarwa ta bidiyo cikin Turanci da ofishinsa ya fitar, Netanyahu ya ce, "Duk da cewa wannan ba shi ne karshen yakin Gaza ba, amma mafarin kawo ƙarshen yaƙin ne."

2024 GMT - Shugaban EU ya ce mutuwar Sinwar 'ta yi matukar raunana' Hamas

Mutuwar shugaban Hamas, Yahya Sinwar "ta yi matukar raunana" Hamas, in ji shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen.

Von der Leyen ta shaida wa manema labarai a Brussels cewa, "mutuwar (Sinwar) tabbas lamari ne da ya yi matuƙar raunana Hamas."

TRT World