Laraba, 16 ga Oktoban 2024
1241 GMT — Lebanon ta shigar da sabon ƙorafi ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin tilasta wa Isra'ila dakatar da hare-haren da take kaiwa nan take tare da janye sojojinta daga yankin na Lebanon.
Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar ta fitar ta ce koken ya bukaci yin Allah wadai da "ci gaba da cin zarafi da Isra'ila ke yi kan kasar Labanon da kuma tilasta mata aiwatar da kuduri mai lamba 1701."
Ma'aikatar ta yi tir da "ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon ta kai hari ta sama da ta ruwa da ta ƙasa, da Isra'ila ke yi, da kuma kai hari kan ofisoshin sojojin Lebanon da motocin daukar marasa lafiya da na agaji, da fararen hula… da kuma dirar wa ƙauyuka da birane."
Ta yi kira ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya yi Allah wadai da ci gaba da ci gaba da nuna kiyayyar da Isra'ila ke yi kan Lebanon da al'ummarta, da kuma mamayar da take yi a kasarta.
1221 GMT — Hare-haren Isra’ila sun kashe akalla shida kan gine-ginen kananan hukumomi a kudancin Lebanon
Ma'aikatar Lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa akalla mutum shida ne suka mutu sannan wasu 43 suka jikkata sakamakon harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai kan wasu gine-ginen kananan hukumomin birnin Nabatie da ke kudancin kasar Lebanon.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce ana ci gaba da neman wadanda suka tsira da rayukansu a karkashin baraguzan ginin.
1210 GMT — Falasdinawa biyu sun mutu a harin da Isra’ila ta kai a Gaza
Akalla Falasdinawa biyu ne suka mutu yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon wani hari da jiragen yakin Isra'ila suka kai kan wata mota a garin Al-Zawayda da ke tsakiyar Gaza, kamar yadda wata majiyar lafiya ta shaida wa Anadolu.