Akalla Falasdinawa tara, da suka hada da yara uku da mahaifiyarsu, aka kashe / Hoto: AP Archive

Alhamis, 17 ga Oktoban 2024

1503 GMT — Akalla Falasdinawa tara, da suka hada da yara uku da mahaifiyarsu, aka kashe tare da jikkata wasu da dama a wani hari da jiragen Isra’ila suka kai a tsakiyar Gaza, in ji wata majiyar lafiya.

Majiyar ta ƙara da cewa, an samu asarar rayuka a lokacin da wani jirgin yakin Isra'ila ya harba makami mai linzami a cikin wani gida da ke sansanin 'yan gudun hijira na Maghazi.

An rusa gidan gaba ɗaya a harin kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana. Ana ci gaba da aikin ceton wadanda suka tsira a karkashin baraguzan ginin.

1303 GMT — Isra'ila ta yi ikirarin cewa mai yiwuwa ta kashe Shugaban Hamas Yahya Sinwar

Rundunar sojin Isra'ila ta ce akwai yiwuwar ta kashe shugaban ɓangaren siyasa na ƙungiyar Hamas, Yahya Sinwar bayan wani hari da ta kai gaza, wanda ta ce ta kai da niyyar samun mambobin ƙungiyar a maɓoyarsu.

Ta ce a wannan matakin, ba za a iya tabbatar da ko su waye ta kashe ba.

0530 GMT — Isra'ila ta kashe ƙarin fararen-hula a hare-haren da ta kai Gaza

Dakarun Isra'ila sun kashe fararen-hula da dama tare da jikkata wasu a hare-haren da suka kai da sanyin safiya a gidajen mutne a Birnin Gaza, a cear kamfanin dillancin labaran Falasɗanawa WAFA.

Hare-haren da dakarun Isra'ila suka kai ta sama da sanyin safiya, sun fada kan gidan iyalan Halou da ke Titin Sinaa a kudu maso yammacin birnin.

Majiyoyi daga asibiti sun tabbatar da mutuwar mutum biyar, yayin da mutane da dama suka jikkata.

An garzaya da mutanen da suka jikkata zuwa wani asibiti da ke kusa, ko da yake ba a san girman raunukan da suka ji ba.

A gefe guda, dakarun Isra'ila sun kai harin bam a gidan iyalan Saleh kusa da maɓulɓular ruwa ta Abu Rashid da ke sansanin Jabalia a arewacin Gaza.

0527 GMT — Hezbollah ta kai hari kan tankokin Isra'ila a Lebanon

Hezbollah ta ce ta kai hari da makamai masu linzami a kan tankoki biyu na Isra'ila a Tuddan Labbouneh da ke kudancin Lebanon, inda ta jikkata dakarun Isra'ila.

0300 GMT — Amurka ta ƙaddamar da jerin hare-haren sama a kan 'yan Houthi a fadin Yemen

Sojojin Amurka sun kai hari a wasu wuraren ajiyar makamai na Houthi a Yemen, in ji manyan jami’an Amurka.

"Wannan wani nuni ne na musamman na ikon Amurka na kai hari kan wuraren da abokan hamayyarmu ke samun mafaka, komai ɓuyan da za su yi a karkashin kasa, komai taurarewar su, ko kuma kangarewar su," in ji Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin a cikin wata sanarwa ranar Alhamis.

"Aikin da sojojin saman Amurka suka ya nuna yadda Amurka za ta iya kai hari a duniya don daukar mataki kan irin wadannan wurare idan ya kama, kowane lokaci, a ko ina."

Wani babban jami'in tsaron Amurka ya shaida wa ABC News cewa, "Rundunar sojin Amurka ta kai hare-hare da dama a kan wuraren ajiyar makamai na Houthi da ke samun goyon bayan Iran a yankunan da ke karkashin ikon Houthi a Yemen."

Amurka ta ƙaddamar da jerin hare-haren sama a kan 'yan Houthi a fadin Yemen

Karin bayani 👇

2340 GMT — Isra’ila ta sake jefa bama-bamai a Lebanon, ta kashe magajin garin Nabatiyeh

Isra'ila ta kai hare-hare da dama a Lebanon, inda ta kashe wani magajin gari, da ruguza gine-gine tare da haddasa barna a yankuna da dama na kudancin kasar.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce jiragen yakinta sun kai hari kan wasu wuraren da kungiyar Hezbollah take a kudancin birnin Nabatiyeh na kasar Lebanon.

Ma'aikatar Lafiya ta kasar Lebanon ta ce mutum 16 ne suka mutu sannan wasu 52 suka jikkata sakamakon harin da aka kai kan wasu gine-ginen kananan hukumomi biyu.

Akalla mutum shida ne suka mutu a wasu hare-haren kamar yadda jami’ai da rahotanni suka bayyana.

Magajin garin Nabatiyeh na cikin wadanda suka mutu, kamar yadda wani jami'in yankin ya shaida wa kamfanin dilancin labaran AFP, ya kuma kara da cewa hare-haren "ya zama wani nau'i na wuta".

TRT World